Mutane tara sun mutu bayan ɓarkewar kwalera a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutane tara ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Sandamu da ke Jihar Katsina sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa da aka fi sani da kwalera a wasu ƙauyuka.

Shugaban ƙaramar hukumar Usman Nalado ya sanar wa manema labarai hakan inda ya ce tuni ya kai rahoton afkuwar lamarin ga hukumar kiwon lafiya a matakin farko.

Ya ce, jami’an hukumar sun ziyarci ƙauyukan da abin ya shafa a ƙaramar hukumar domin gane wa idanunsu.

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu da Daura, Aminu Jamo ya kai tallafin kayan abinci da kuɗi don a raba wa waɗanda abin ya shafa .

Haka ma, Kakakin Majalisar Dokoki na jihar, Nasiru Yahaya da Aminu Jamo sun kai ziyarar jaje tare da bayar da nasu tallafin.

By Babaji