
Daga BELLO A. BABAJI
Kira da ɓangaren jami’yyar APC ƙarƙashin jagorancin tsoffin gwamnonin Zamfara, Bello Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari suka yi na a sanya dokar ta-ɓaci jihar, alamu ne da ke nuna ƙiyayyarsu a fili game da ayyukan ci gaba da aka samu ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare.
Wata takarda da Sakataren hulɗa da jama’a na PDP, Halliru Andi ya fitar, ta ce jam’iyyar PDP ta mayar da hankali wajen gyara ɓarnar da gwamnatocin APC ta yi na tsawon shekaru 25 wanda hakan ya nuna yadda nasarorin gwamna Dauda Lawal suka zama barazana ga APC a yunƙurinta na raina ƙoƙarinsa saboda cimma manufofin salon siyasarsu ta 2027.
Ya ce, kira ga sanya dokar ta-ɓaci da jami’yyar ta yi ba shi da asali kuma rashin mutunta al’ummar Zamfara ne, saboda APC ta kawar da kai daga kurakuran gwamnatin Matawalle inda salonsa mara tsari na kawar da ƴan ta’adda ya ƙunshi samun kusanci da jagorancinsu, ya na mai cewa gwamnatin Matawalle ta gaza tabbatar da tsaro wanda hakan ya faru ne sakamakon bada mafaka, samar da motocin Hilux da bada lada na kuɗi ga ƴan bindiga tare da ba su damar zirga-zirga a gidan gwamnatin jihar.
Andi ya ce, saboda haka ne al’ummar jihar suka ɗanɗana kuɗarsu kasancewar ƴan bindiga na kai hare-hare a garuruwa domin su na samun mafaka na gwamnati.
Ya ƙara da cewa, zargi ne mara tushe a ce Gwamna Lawal ya na dakatar da yaƙi da ayyukan ta’addanci a Zamfara inda ya ce hakan yunƙuri ne na siyasantarwa da kuma raina ƙoƙarinsu na warware matsalolin taɓarɓarewar tsaro a jihar, ya na mai cewa samar da tsaro shi ne babban burin Lawal Dare kasancewarsa gwamna na farko da ya fifita tsaro sama da komai a jihar.
Har’ilayau, Sakataren ya ce, gwamnatin Dauda Lawal ta ɗauki ƙwararan matakai da suka haɗa da samar da jami’ai na garuruwa (CPG) da gidauniyar kuɗi na tallafa wa jami’an tsaro duk don tabbatar da an kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a faɗin jihar inda a kwanakin baya gwamnan ya raba motocin sintiri ga jami’an.
Kazalika, ya ce Matawalle bai taɓa neman Gwamna Lawal ba da sunan su haɗa hannu wajen magance ayyukan ta’addanci a matsayinsa na ƙaramin ministan tsaro wanda hakan ya nuna rashin ƙwarewa da tausayawa ga al’ummar Zamfara.
Sakataren a madadin jami’yyar ya ce, su na kira ga Shugaba Bola Tinubu ya tsige Bello Matawalle a matsayin ƙaramin ministan tsaro a Nijeriya saboda rashin cantatarsa da kuma ayyukansa na baya waɗanda ba iya raina ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci suka yi ba, har ma sanya zaman lafiyar ƴan ƙasa suka yi acikin haɗari.
Bugu da ƙari, yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi bincike kan ayyukan Matawalle musamman kan alaƙarsa da shugabannin ƴan bindiga.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga APC ta mayar da hankali kan muhimman ababen da su ke damun Zamfara madadin ƙirƙirar zarge-zarge marasa tushe da kuma ababen da ka iya tada zaune-tsaye.
