
Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da ake cigaba da ƙirga ƙuri’u da aka kaɗa a zaɓen gwamnan jihar Edo a ranar Asabar, ɗan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebholo ya na kan gaba.
Sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi 16 cikin 18 na jihar kamar yadda hukumar zaɓe, INEC ta sanar, Okpebholo ya samu ƙuri’u 244,549 yayin da takwaransa na jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo ke na biyu da ƙuri’u 195,954.
Olumide Akpata na jam’iyyar LP ya samu ƙuri’u 13,348.
Kawo yanzu INEC ta je hutun sa’o’i uku don jiran sakamakon zaɓen sauran ƙananan hukumomi biyu da suka rage.
