Zaɓen Edo: Wakilin PDP ya zargi INEC da haɗa kaso 90 na ƙuri’un ƙarya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Edo, Osiagbovo Iyoha ya tada batun zargi mai ƙarfi game da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ake gaf da sanar da wanda ya yi nasara.

Iyoha wanda shi ne wakilin jam’iyyar PDP a jihar, ya yi zargin cewa kashi 90 na sakamakon zaɓen daga hukumar zaɓe, INEC ya ke, ya na mai cewa ƙirƙirar sakamakon aka yi.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da a ke shirin karɓar sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Etsako ta Tsakiya wanda kuma shi ne na ƙarshe.

Ya ce, akwai wata jami’iyyar da ke da iko game da sakamakon zaɓen, ya na mai cewa sakamakon ya na tafiya ne ba yadda al’ummar jihar suka so ba.

Wannan zargi da wakilin jam’iyyar ya yi ya haifar da cecekuce a cikin al’umma game sakamakon zaɓen.

Kawo yanzu dai jami’yyar APC ke kan gaba yayin da PDP ke ta biyu.

By Babaji