
Daga BELLO A. BABAJI
Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta yi watsi da ƙara da ke neman a tsige Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa.
Ƙungiyar ƴan APC reshen Arewa-ta-Tsakiya ta ƙalubalanci naɗa Ganduje da aka yi a muƙamin kasancewar shi ba ɗan yankin ba ne.
Cikin ƙarar mai ɗauke da lamba kamar haka; FHC/ABJ/CS/599/2024, an shigar da Ganduje, APC da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC inda ɓangaren shigarwar ya buƙaci a hana Ganduje cigaba da kiran kansa shugaban jam’iyyar.
Sannan, ƙarar ta nemi kotun ta umarci INEC ta rushe da duk wani hukunci da ta yi tun daga ranar 3 ga watan Agusta, 2023, lokacin da Ganduje ya fara jagorancin jami’yyar, ciki har da tarurruka, zaɓen fidda gwani da wasu naɗe-naɗe da aka yi.
Don haka, ƙarar ke ikirarin cewa Ganduje na shugabantar APC ne ta haramtacciyar hanya tunda ba ya daga cikin ƴan Arewa-ta-Tsakiya.
Haka kuma ƙarar ta nuna cewa, Majalisar Zartarwa (NEC) ta jami’yyar ta karya dokar jami’yyar kasancewar ta maye gurbin Abdullahi Adamu da ya zo daga Arewa-ta-Tsakiya da Ganduje da ya zo daga Arewa-maso-Yamma.
A lokacin da ya ke hukunci kan ƙarar, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce ɓangaren shigar da ƙarar ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ƴan APC na Arewa-ta-Tsakiya, Alhaji Sale Zazzaga, ba su da hurumin shigar da ƙarar, ya na mai cewa ƙungiyar ba ta da ingantacciyar shaida da ke nuna ta yi rijista da Hukumar Harkokin Rijista (CAC).
Alƙlin ya ce, za a iya tsige Ganduje ne ƙadai yayin da aka samu tattaunawa a mataki na ƙasa.
Bugu da ƙari, lauyan ɓangaren ƙarar, Ayuba Abdul ya ce za su ɗaukaka hukuncin ƙarar.
