Tinubu da Ganduje sun yaba da nasarar APC da kammala zaɓe cikin lumana a Edo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Monday Okpebholo na jami’yyar APC kan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Edo da aka yi a ranar Asabar.

Hukumar zaɓe, INEC ta sanar da nasarar ɗan takarar na APC bayan ya doke abokanan takararsa.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa shugabannin APC a mataki na ƙasa, manyan Jihar Edo da gwamnonin jami’yyar wajen aiki tuƙuru don ganin an cimma nasara.

Ya ce, nasarar ta nuna yadda al’ummar ke goyon baya jami’yyar mai mulki da ayyukanta na ci-gaba da shirye-shirye na inganta tattali don bunƙasa al’ummar Nijeriya.

Ya yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan da kar ya yi tunƙaho da nasarar da ya samu, a madadin haka ya fuskanci ƙalubalen da ke gabansa na jagoranci.

Har’ilayau, Shugaba Tinubu ya jinjina wa sauran ƴan takarar da suka fafata a zaɓen kan gudunmawarsu ga ci-gaban demokraɗiyya a Nijeriya, ya na mai cewa yin zaɓen cikin lumana ya nuna yadda demokraɗiyya ke ƙara tabbatuwa a ƙasar.

Haka ma Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya Sanata Okpebholo murnar nasarar tasa.

Cikin wata takarda da Sakataren Labaransa, Edwin Olofu ya fitar, Ganduje ya ce nasarar wata shaida ce da ke nuna cewa al’ummar jihar sun amince da kyawawan manufofi da ake da shi wa jihar da na gwamnatin Shugaba Tinubu a mataki na ƙasa.

By Babaji