Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ibtila’in ambaliyar ruwa na Maiduguri a jihar Borno ya fito da bayanai da yawa-yawan mu ba mu sani ba. Labarun jihar Borno na nuna yanki ne mai zafin rana da kuma makwabtaka da hamada. Duk da haka a na da bayanan kifin Baga da kogin tafkin Chadi. Aukuwar ambaliyar ta fito da labarin DAM ko madatsar ruwan Alau da hukumomi su ka ce fashewar ta ne ta jawo ambaliyar ko da ma daga farko an ce wa imma buɗe ruwan a ka yi a lokaci daya ko kawai wata ƙaddara ce ta sa ruwan ya tumbatsa ya shigo matsugunan jama’a. Koma dai me ya faru yanzu mun game akwai Alau da ke da tarin ruwa da ba mamaki a ka kafa don bunkƙasa noman rani da ban ruwan dabbobi.
Madatsun ruwa kan zama alheri a yankunan da a ƙaƙafa su. A jihar Gombe madatsar ruwan Dadin Kowa ta zama babban alheri ga al’ummar yankin da kan yi noma, kama kifi da sauran sana’o’I da su ka shafi bakin kogi. Bayan haka ma daga nan babban birnin jihar ke samun ruwan famfo da hakan ya rage matsalar karancin ruwan sha musamman a shekarun baya. Ga kogin Numan a jihar Adamawa da duk mai ziyartar Yola zai bi saman gadar da ta ratsa ruwan inda mutane kan amfana da arzikin kogi. Shiga jihar Taraba ma mai kogin Donga inda noman rani ya zama hanyar arziki ga ɗimbin jama’a. Ina ma mutum ya shigo Makurdi a jihar Binuwai ya ga yanda kogi ya ratsa birnin gwanin sha’awa. Kogin Hadeja da Jama’are a jihar Buachi da Jigawa da ruwan da ya ratsa Gashua a jihar Yobe na zama hanyar samun abinci ga jama’a. Ba kuma sai ma an kafa madatsar ruwa ba idan mutum ya bi ta Wudil a jihar Kano da Dindima a jihar Bauchi zai ga yadda ruwan damuna ya ratsa manyan kwarurrukan garuruwan inda hark wale-kwale ke shawagi.
Na halarci taruka da daman a hanyoyin da za a bi don yashe kogin tafkin Chadi da ke tsulancewa tsawon shekaru bisa ƙalubalen sauyin yanayi. Ga labarun share ciyawar nan ta kachalla da ke kawo tarnaki ga tafkin. Rashin ƙarfin tafkin na barazana ga mazauna gabar tafkin don taɓa lamuran noman rani, kamun kifi da ban ruwan dabbobi. Arziki ne Allah madaukakin Sarki ya horewa al’umma inda su kuma al’ummar bisa wasu ɗabi’un su kan kawo tarnaki ga arzikin da su ka gada kaka-da-kakanni. Ruwa babban arziki a duk inda ya ke don jama’ar da ba ta da ruwa kan zauna cikin damuwa dare da rana. Wani arzikin daga Allah ga Nijeriya shi ne ƙasar na cikin ƙasashen duniya da ke da iyaka da teku.
Wannan rahama ce da kan taimakawa wajen sufurin jiragen ruwa da kan yi jigilar kayan kasuwanci daga sassan duniya. ƙasashen da ba su da iyaka da bakin teku kan matso zuwa cikin ƙasashe masu teku don samun kayan da a kan yi safarar su masu ɗimbin yawa na kasuwa daga manyan ƙasashen duniya. Kasancewar iyakar tekun na yankin kudancin Nijeriya ne sai hukumar kula da hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa ƙarƙashin tsohon shugaban hukumar Malam Hassan Bello ta kirkiro wasu tashoshin sauke hajar teku na kan tudu da a ke kira tashar tsandauri a Kano. An kaddamar da tashar a Kaduna hakanan an kafa wata a Funtua jihar Katsina sai kuma share fili don kafa tashar a Potiskum jihar Yobe wanda aikin ya sanya al’umma farin ciki. Aikin tashoshin shi ne kawo hajar teku zuwa tashoshin ta hanyar jiragen ƙasa da ke haɗe da tashoshin ko kuwa manyan motocin sufuri. Mazauna nesa da teku ba sa buƙatar sai sun tafi Lagos kafin samun hajar da su ka yi sauti ko kuma hajar da su ke son turawa ƙetare don sayarwa.
Rashin bin ƙa’idoji na mu’amala da irin koguna ko madatsun ruwan da ke daf da matsugunan jama’a na kawo asarar rayuka baya ma ga batun ambaliyar ruwa. Yara masu wanka a koguna ba tare da kular manya ba kan iya nitsewa su rasa ran su. Dorinar ruwa ma kan fito a wasu sassan ta kai farmaki ga mutane ko lalata gonaki. Akwai rahotanni masu nuna tsatsuba tsakanin wasu masunta da kan haddasa matsala ga abokan sana’ar su. Wasu kogunan ba sa rasa zama matsuguni ga aljannu.
Rahotanni na bayyana mutuwar fiye da manoma 40 a yankin karamar hukumar Gummi da ke jihar Zamfara.
Akasin ya faru a karshen makon jiya lokacin da manoman su ka shiga kwale-kwale don ketara kogi.
Kazalika, rahotannin sun kara da cewa manoma 53 ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da akasin ya auku inda a ka samu ceto mutum 12.
Ba wani sabon abu ba ne samun hatsarin kwale-kwale da a kan ɗorawa lodi fiye da kima da kuma rashin sanya rigar alamar hatsari ta ruwa.
Hukumar kula da ruwa da dukkan kogunan Nijeriya ta baiyana shirin faɗaɗa madatsun ruwa musamman da ke daf da birane don rage ambaliyar ruwa.
Waɗannan matakan sun biyo bayan fashewar madatsar ruwan Alau da ke jihar Borno da ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya.
Shugaban hukumar ruwan da koguna Umar Ibrahim Muhammed wanda ya duba dam ɗin da ya malale Maiduguri ya ce ya baza ma’aikatan sa a dukkan faɗin Nijeriya don duba koguna da rubuta rahoton halin da su ke ciki.
“Yanzu haka duk ma’aikata na sun tashi su na nan haikan wanda mu na tsammanin a cikin wannan satin da za mu shiga Insha Allahu kowanen su zai gabatar da sakamakon binciken da su ke kan yi yanzu”
Umar Muhammad ya kara da cewa za a rage ƙarfin ruwan wasu koguna ta hanyar bunƙasa noman rani da gina wasu kananan madatsun ruwan da za a riƙa tura ruwan kogin da ke neman tumbatsa.
Game da madatsar ruwan da ta haddasa ambaliya a Maiduguri, Umar ya ce ruwan ne ya fi ƙarfin madatsar kuma tushen sa daga tsaunukan Mandara ne a kan iyakar Nijeriya da Kamaru “Mandara MOUNTAIN na tsakanin Nijeriya da Kamaru. Ta ɓangaren da ya ke cikin Nijeriya ta nan ruwan ke gudanowa”
Masanin kimiyyar siyasar tattalin arziki na jami’ar Abuja Dr.Farouk BB Farouk ya aza alhakin ambaliyar ta Borno da sakaci da kuma rashin ɗaukar matakai a baya ga waɗanda kan yi sako-sako da alhakin da ke wuyansu “saboda haka wane ne ya ƙi ɗaukar matakin a zubar da ruwa ko da kadanne don ka da wannan gurin ya fashe”
Duk shekarar da a ka samu yawan ruwan sama a kan samu ambaliya a sassan Nijeriya da kan faru bisa wasu dalilan ma da su ka haɗa da sauyin yanayi sanadiyyar hayaƙi da ke gurbata muhalli, sare bishiyoyi, toshe magudanan ruwa da gina gidaje kan ƙwazazzaban da ruwan damuna ke bi.
A na cigaba da kiran ba da tallafi ga al’ummar Maiduguri a jihar Borno biyo bayan ambaliyar ruwa yayin da shugaba Tinubu ya ziyarci jihar don jaje.
Ambaliyar ruwan daga ɓallewar madatsar ruwan Alau ta haddasa asarar dukiya da rayuka da tilasata mutane da dama ƙaura zuwa sansanonin gudun hijira.
In za a tuna gabanin ziyarar mataimakin shugaban Kashim Shettima ya je Maiduguri da alwashin tallafin motocin shinkafa.
Shugaba Tinubu ya zaga har fadar Shehun Borno da duba jama’ar da ke zaune a sansanonin inda ya ce zai jagoranci kafa wata gidanuiya don tallafawa waɗanda irn wannan ibtila’I ya shafa.
Bola Tinubu ya kara da cewa ba tabbas ko a ce akwai bazarnar aukuwar irin wannan ambaliya a sassan Nijeriya don yanda a ke samun sauyin yanayi.
Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da ke tare da shugaban ya yi alwashin majalisa za ta haɗa kai da sashen zartarwa wajen kafa gidanuiyar.
Masu sharhi na bukatar sanya ido kwarai ga yadda za a rika raba gudunmawa don tabbatar da cewa waɗanda su ka cancanta ne su ka samu tallafin.
Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya bukaci a samu haɗin kai na bai daya don tunkarar yaƙi da sauyin yanayi.
Shettima na magana ne a Gombe a taron da hukumar raya arewa maso gabar ta shirya don ƙarfafa dabarun kare yanayi.
Kashim Shettima ya ce ba wanda ya tsira daga wannan barazana ta sauyin yanayi da kan raba mutane da dukyar su.
Musamman a yankin arewa maso gabar, Kashim ya ce jama’a sun ga illar yadda sauyin yanayin kan kawo ƙalubale na samuwar ibtila’i.
Hakanan Shettima ya ce Nijeriya za ta kara azama wajen tabbatar da nasarar dakatar da gurɓata yanayi a duniya zuwa shekara ta 2060 don aminta duniya daga sauyin yanayi.
Kammalawa;
Lokaci ya yi da jama’a za su rungumi wasu hanyoyi na samun makamashi don rage gurbata yanayi da kan ta’azzara sauyin yanayi. Gwamnatocin duniya musamman na ƙasashe masu masana’antu na da haƙƙin ɗaukar matakan kare yanayi don kusan su ne gagaruman masu gurɓata yanayin. Kazalika a riƙa kula da madatsun ruwa don hana su tumbatsa. Wani abun kuma mutane su riƙa ƙoƙarin zama a sassan ba baraznar ambaliya. Haƙƙin gwamnatine kai ɗaukin gaggawa ga wanda ibtila’in ambaliya ta shafa. Masu hannu da shuni kan iya taimakawa ga jama’ar da ke cikin buƙata amma ta kokarin miƙa tallafin kai tsaye ga jama’a zai fi yin tasiri.
