Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wazirin Katsina na 5 farfesa Sani Abubakar Lugga yayi kira ga hafsoshin ƙasar da su sauka daga muƙamin su saboda gazawar su wajan kare rayukan al’ummar ƙasan.
Ya ce sai a mayesu da ƙwararrun sojojin da za su iya magance matsalar rashin tsaro a ƙasar musamman a arewacin Nijeriya .
Farfesa Sani Lugga ya yi kiranne a jawabin sa wajen taron da ƙungiyar ‘yan jaridu na ƙasa reshen Jihar Katsina ta shirya a cikin bukukuwan cika shekara 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina.
Ga masu kiraye kiraye na jama’a su tashi tsaye su kare kansu waziri yace babu wata ƙasa da ta taɓa yin wannan gangancin domin haka zai ƙara kawo rashin tsaro a ƙasar.
Ya bayyana cewa kare rayukan al’ummar ƙasa na hannun sojoji da yan sanda wanda dole su tashi tsaye wajan tabbatar da haka
Idan sojoji ba zasu iya kare rayukan al’ummar ba to abar jihohi su kafa jami’an tsaro na kansu.
A jawabin sa mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe ya yabawa ƙungiyar ‘yan jarida reshen jihar da suka shirya irin wannan taro da kira a garesu da su rinƙa gudanarwa akai akai
Ya tabbatar wa ƙungiyar cewa gwamnatin jihar Katsina zata haɗa kai da ƙungiyar wajen ciyar da jihar gaba.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar da aikace aikace da dama akan harkar ilimi,wajan kiwon lafiya da samar da ayyukan yi da sauransu.
Shi ma a nasa jawabin shugaban ‘yan jaridu reshen jihar malam Tukur Ɗan Ali ya bayyana cewa irin wannan taron zai baiwa gwamnati damar sanin irin nasarorin da ta samu da inda aka tsaya da kuma inda aka dosa
Ya yabawa gwamnatocin baya a bisa irin gagarumar ayyuka da suka aiwatar a jihar a shekara 37 da ƙirƙira.
An gabatar da ƙasidu daban daban a ciki akwai ƙasida da aka gabatar akan rayuwa da gwagwarmaya da tsohon malamin tarihi marigayi Dr Yusuf Bala Usman na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya sha a lokacin yana raye.
