Majalisar dokokin Katsina ta buƙaci akai jami’an tsaro Kankia

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar dokoki ta jihar Katsina ta buƙaci akai jami’an tsaro cikin gaggawa a wasu garuruwa da ke ƙaramar hukumar Kankia.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kankia, Hon Salisu Hamza Rimaye, ya gabatar da ƙudirin a zauren majalisar.

Ya buƙaci abokan aikinsa a zauren najalisar su goya masa baya a turawa ɓangaren zartarwa domin a samar da tsaro a wasu garuruwa guda shida da ke ƙaramar hukumar.

Garuruwan sun haɗa da Tasha Fanni, Malamawa, Tudun wulli, Walwala, Sukuntuni da Magani.

Da yake gabatar da ƙudirin a zauren majalisar ɗan majalisar ya nuna rashin jin daɗinsa na yadda Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dr Nasir Mu’azu Ɗanmusa, na rashin ɗaukar wayar shi a lokaci da wasu mahara su ka yi ƙoƙarin shiga cikin ƙauyukan.

Haka kuma ya buƙaci a sanya mazaɓarsa cikin jerin ƙananan hukumomin da za a ɗauki jami’an tsaro na KCWC, domin samar da tsaro a yankin wanda haka zai rage yaɗuwar ta’addanci a sassan ƙaramar hukumar.

Shi kuwa ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kusada, Hon Ghali Garba, ya sake gabatar da ƙudirin tunatarwa na sake gina hanyar karkara wadda ta tashi daga Dunduni, Jofalawa, Zango zuwa Makadawa.

By ukarofi