Raɗɗa ya gwangwaje ma’aikata da kyautuka a bikin cikar Katsina shekaru 37

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya bayar da kyautuka ga wasu daga cikin ma’aikatan jihar 14, waɗanda suka fi nuna ƙwazo a yayin gudanar da ayyukansu.

Gwamnatin jihar ta ƙaddamar da bayar da kyautukan ne a wurin cin abincin dare da aka shirya albarkacin cikar jihar shekaru 37 da kafuwa.

An ƙirƙiri Jihar Katsina ne a lokacin mulkin soji ƙarƙashin shugabancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1987.

A yayin da wasu daga cikin ma’aikatan suka samu kyautukan motoci, wasu kuwa sun samu kyautar kuɗaɗe.

Waɗanda aka bai wa kyautar motocin sune; Lawal Halilu daga ma’aikatar ilmi, Abubakar Lawal daga ofishin binciken kuɗi, Bishir Aliyu daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, Farida Nuraddeen malamar firamare daga ƙaramar hukumar Bakori.

Waɗanda kuwa aka karrama da kyautar kuɗi har Naira miliyan biyu ga kowannen su sun haɗa da; Nura Idris na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, Nura Isiyaku na hukumar ɗaukar malamai, Mansur Suleiman daga hukumar raya karkara ta jihar (KTARDA), da Shema’u Kabir daga hukumar SPHCDA.

Sauran sun haɗa da; Abdullahi Yusuf, Abdullahi Muhammad, Mu’awiyya Musa, Isuhu Ahmed, da kuma Sada Rabe waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi daban-daban.

Da ya ke jawabi a wajen taron, gwamna Raɗɗa ya gode wa Allah da Ya azurta jihar da shugabanni na gari waɗanda suka kawo ci-gaba tun daga kafuwar ta.

By Babaji