Gwamnatin Tarayya ta sake maka tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello kotu

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume guda 16 kan Yahaya Bello, tsohon gwamnan Jihar Kogi, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito.

An shigar da tuhume-tuhumen ne a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba, kuma suna kan zargin wawashe kuɗaɗe har Naira biliyan 110,446,470,089, wanda ya saɓawa sassa na 96 da 311 na dokar Penal Code na Arewacin Nijeriya na 1963, kuma akwai hukunci ƙarƙashin sashe na 312 na wannan doka.

Tsohon gwamnan, wanda shine kawai wanda aka tuhume shi a cikin tuhume-tuhume guda 19 da hukumar EFCC ta shigar masa a baya, zai fuskanci wannan sabuwar tuhume-tuhume guda 16 tare da wasu jami’an gwamnatin Jihar Kogi guda biyu, Abdulsalami Hudu da Umar Oricha.

An zargi masu laifin da yin amfani da kuɗaɗen Jihar Kogi don siyan kadarori a wurare masu tsada a cikin babban birnin tarayya Abuja da kuma Dubai kamar yadda takardar tuhumar ta bayyana.

Tuhumar farko ta tuhume Bello, Oricha da Hudu, a wani lokaci a shekarar 2016 a Abuja, sun yarda tsakaninsu “da aikata laifi na cin amana da ya shafi jimlar kuɗi Naira biliyan 110,446, 470, 089.00 wanda aka amince musu.

A tuhumar biyu, an ce sun yi amfani da jimlar kuɗi Naira miliyan 950 a shekarar 2023 “domin sayen kadarar da aka sani da No, 35 Danube Street, Maitama District, Abuja”.
Tuhumar ta uku ta zarge su da yin amfani da Naira miliyan 100 “domin sayen kadarar da aka sani da No, 1160 Cadastral Zone CO3, Gwarimpa I District, Abuja” a shekarar 2021.

A tuhumar ta huɗu, an zarge su da amfani da Naira miliyan 920 domin sayen kadarar da aka sani da No, 2 Justice Chukwudifu Oputa Street, Asokoro, Abuja a shekarar 2020.

A tuhumar biyar, an zarge su da amfani da Naira miliyan 170 domin sayen kadarar da aka sani da Block D Manzini Street, Wuse Zone 4, Abuja a shekarar 2022.

A tuhumar ta shida, an zarge su da yin amfani da Naira miliyan 100 domin sayen kadarar da aka sani da No,1773 Guzape District, Abuja a shekarar 2018.

Tuhumar ta bakwai na zargin su da amfani da Naira miliyan 100 domin sayen kadarar da aka sani da No, A02/176 Block 488B, Lome Street, Wuse 1, Abuja a shekarar 2020.

A tuhuma ta takwas, an ce a shekarar 2020, sun yi amfani da Naira miliyan 66 domin sayen kadarar da aka sani da No, 739 Aminu Kano Crescent, Wuse 2 a No 13 Citiscape-Sharriff Plaza, Abuja.

Tuhumar ta tara ta zarge su da amfani da Naira miliyan 550 domin sayen kadarar da aka sani da No, 2934 A Cadastral Zone A06 wanda aka fi sani da No,1 Ikogosi Spring Close, Maitama District, Abuja, a shekarar 2020.

A tuhuma ta goma, an ce sun yi amfani da Naira miliyan 650 domin sayen kadarar da aka sani da No, 1058, mai girman 1450.77 sqm a Cadastral Zone A08, Wuse 2 wanda aka fi sani da No, 2 Durban Street Abuja, a shekarar 2021.

A tuhumar ta goma sha ɗaya, an zarge su da amfani da Dirham 5,698,888 a shekarar 2022 domin sayen kadarar da ke Hotel Apartment Community, Burj Khalifa, dake Plot 160, Municipality NO 345-7562, Sky View Building No.401, Floor4 a Dubai”

Tuhumar ta goma sha biyu ta zarge su da yin amfani da Naira miliyan 60 domin sayen kadarar da aka sani da Block 18 (337) Flat B Gwelo Street, Wuse Zone 4, Abuja a shekarar 2016.

A tuhuma ta goma sha uku, an zarge su da yin amfani da jimlar kuɗi Naira miliyan 310,443,450.00 don gyara kadarar da aka sani da No, 9 Benghazi Street, Wuse Zone 4, Abuja a shekarar 2017.

Tuhuma ta goma sha huɗu ta zarge su da aika jimlar kuɗi Dala 570,330.00 zuwa asusun lamba 4266644272 dake TD Bank, Amurka a shekarar 2021.

A tuhuma ta goma sha biyar, an zarge su da aika jimlar kudi Dala 556,265.00 zuwa asusun lamba 4266644272 dake TD Bank, Amurka, a shekarar 2021.

A tuhuma ta goma sha shida, an zargi Bello shi kaɗai da kasancewa yana da jimlar kuɗi Naira miliyan 677, 848,000 da aka samu ta haramtacciyar hanya daga Bespoque Business Solutions Limited a wani lokaci tsakanin 2017 da 2018 a Abuja.

Ola Olukoyede, shugaban EFCC, daga baya ya zargi Bello da ciro Dala $720,000 daga asusun Jihar Kogi domin biyan kuɗin makarantar ɗansa na gaba.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma shigar da tuhume-tuhume guda 19 kan Bello akan zargin halasta kuɗin haram.

Duk da haka, shari’ar ta ci gaba da samun tsaiko a lokuta daban-daban saboda rashin halartar tsohon gwamnan.

A ranar 20 ga watan Agusta, kotun ɗaukaka ƙara ta umarci Bello da ya miƙa kansa don a gurfanar da shi.

By ukarofi