Kotu ta yi watsi da buƙatar APC ta hana zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ƙi amincewa da buƙatar da jam’iyyar APC ta shigar na neman hana hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar 26 ga watan Oktoba.

Masu ƙarar su ne Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC ta hannun lauyansa, Mustapha Idris, inda su ka shigar da ƙara a ranar 18 ga watan Satumba tare da miƙa ƙorafin a ranar 20 ga watan Satumba.

Su na neman kotu da ta hana KANSIEC gudanar da zaɓukan tare da bayar da umarni ga dukkan ɓangarorin biyu da kada su yi wani yunƙuri na gudanar da wani abu tukunna.

Waɗanda ake ƙara sun haɗa da KANSIEC, Majalisar Dokokin Jihar Kano, Babban Lauyan Jihar Kano, INEC, DSS, Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano da Kwamandan NSCDC na Jihar.

Sauran sun haɗa da Anas Muhammad-Mustapha, Farfesa Sani Lawal-Malumfashi, Mukhtar Garba-Dandago, Isyaku Kunya, Shehu Kura, Kabiru Zakirai da Aminu Inuwa-Fagge.

Mai shari’a Simon Amobeda, ya ki karɓar roƙon,  inda ya kamata masu ƙorafin su sanar da waɗanda suke ƙara domin su nuna dalilin da ya sa ba za a karɓi roƙonsu ba.

Kotun ta kuma amince da a gaggauta sauraran ƙarar.

Amobeda ya ɗage zaman ƙarar har zuwa ranar 4 ga Oktoba domin sauraren ƙorafin.

By ukarofi