Matsin Rayuwa: Na san ku na jin jiki, amma ina daf da sama muku mafita mai ɗorewa — Tinubu ga ƴan Nijeriya

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ƴan Nijeriya ƙudirin gwamnatinsa na samar da mafita mai ɗorewa domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da suke ciki.

Ya bayar da tabbacin ne a jawabinsa da ya yi wa ƴan ƙasa kan bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ƴancin-kai.

“Ina sane da halin ƙunci da dayawa daga cikin ku ke fuskanta a cikin waɗannan lokuta masu ƙalubale.

“Gwamnatinmu ta san cewa yawancinku suna fama da tsadar rayuwa da neman aiki mai tsoka. Ina so in tabbatar muku cewa ina jin koken ku,” inji shi.

Tinubu ya roƙi ƴan Nijeriya da su yi haƙuri “yayin da gyare-gyaren da muke aiwatarwa ke nuna alamun nasara, kuma mun fara ganin haske a gaba.”

By Babaji