Ranar ‘Yancin Kai: ‘Yan sanda da masu zanga-zanga sun yi arangama a Abuja da Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake bikin cikar shekaru 64 da samun ƴancin-kai a Nijeriya, wasu masu zanga-zanga sun fito kan tituna a Jihohin Abuja da Legas don nuna damuwa kan halin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.

Blueprint ta ruwaito cewa a yayin hakan ne masu zanga-zangar suka yi artabu da jami’an tsaro.

Omoyele Sowore, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC shi ya jagoranci zagayen a Legas.

Ƙungiyoyin al’umma da dama suka shirya zanga-zangar wadda sun yi makamancin ta a kwanakin baya game da halin tsadar rayuwa da al’umma ke ciki a Nijeriya.

Manufar yin hakan sune don a warware matsalolin tashin farashin fetur, kayan abinci da sauran ababen gudanar da rayuwa acikin al’umma.

Haka ma a Abuja, mutane da dama ne suka fito daga wurare daban-daban inda aka baza jami’an tsaro a wasu zaɓaɓɓun titina musamman waɗanda ke kai wa zuwa filin ‘Eagle Square’ wanda a nan ne ake taron murnar ƴancin kan.

Daga nan ne jami’an suka watsa borkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar.

By Babaji