NLC ta aika wa ma’aikata saƙo na musamman yayin da Nijeriya ke bikin cika shekara 64 da samun yancin kai

Spread the love

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman ma’aikata da su cigaba da hakuri da halin matsi da ƙasa ke ciki.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ya fitar domin bikin cika shekaru 64 da samun yancin kai na Nijeriya, Joe Ajaero ya fitar ya bayyana goyon bayansa ga ‘yan ƙasa baki ɗaya tare da ma’aikata domin jajircewar su da sadaukar kai a wannan yanayi duk da rashin cika alƙawura daga ɓangaren yan siyasa.

Ajaero ya buƙaci yan gwagwarmaya da su cigaba da jajircewa domin da haka ne kawai za a samu abinda ake buƙata daga wajen gwamnati. Ya jaddada musu cewa yana tare dasu a duk abinda za su gudanar matuƙar bai saɓawa doka ta ƙasa ba.

Ya cigaba da jaddadawa cewa a yanzu dai ta tabbata yan siyasa ba za su taɓa yin abu ba har sai an tilasta musu ba.

Daga ƙarshe Ajaero yayi kira ga yan siyasa da su dawi kan turba na dimukraɗiya domin hakan ne kaɗai zai kawo cigaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar.

By ukarofi