Iran ta kai wa Isra’ila hare-haren makamai masu linzami

Spread the love

Rundunar sojin Isra’ila ta ce Iran ta ƙaddamar mata da hare-hare masu linzami.

Sanarwar da rundunar sojin Isra’ila ta fitar, ta ce hare-haren sun fito ne daga Iran.

Iran ta tabbatar da ƙaddamar da hare-haren kan Isra’ila, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar Iran ya tabbatar.

Isra’ila ta buƙaci ƴan ƙasarta su kasance cikin shiri tare da neman wurin fakewa idan har sun ji ƙara ta gargaɗi.

Masu aiko da rahotanni sun ce an kakkaɓo wasu makaman a sararin samaniyar Jordan.

Kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun ce harin makamai masu linzami kusan 100 Iran ta harbo.

Sai dai rahotanni sun ce Amurka ta taimaka wa Isra’ila wajen kakkaɓo makaman kafin isa Tel Aviv.

Bayanai sun ce wasu makaman da Iran ta harbo sun faɗa yankunan Falasɗinawa

By Babaji