Daga USMAN KAROFI
Mutanen Kano sun yi watsi da zanga-zangar da ake yi a ƙasa baki daya, inda suka ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.
Zanga-zangar ta ɗaya ga Oktoba, 2024, mai taken “FearlessInOctober”, an ingiza ta ne ta kafofin sada zumunta, wata biyu bayan zanga-zangar #EndBadGovernance na watan Agusta.
Zanga-zangar guda biyun suna da kamanceceniya, inda matasa masu fushi ke buƙatar a janye cire tallafin man fetur da ƙarin farashin wutar lantarki.
Da yake lura da halin da ake ciki a Kano, wakilinmu ya ruwaito cewa duk da an ayyana ranar a matsayin hutu, mutane da dama sun zauna a gidajensu.
Sai dai wasu sun fita domin gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
Manyan tituna sun yi shiru ba tare da cunkoso mai yawa ba, yayin da shaguna da wasu ƙananan kasuwanci suka buɗe.
Bincike cikin manyan kasuwanni kamar Kwari, Sabon Gari, Singer da Kurmi ya nuna cewa mafi yawan shaguna a buɗe suke, sai kaɗan ne kawai suka rufe.
A lokacin haɗa wannan rahoton, babu wani alamar zanga-zanga da ke faruwa a ko’ina a cikin jihar.
