Gwamnatin Tinubu ta bai wa ƙananan ƴan kasuwa tallafin N150,000

Spread the love

A jiya Alhamis ne Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da Cibiyar Ƙanana da Matsaƙaitan Sanao’i a Jihar Enugu.

Cibiyar, ita ce irinta ta biyar da Kashim Shettima ke ƙaddamarwa a faɗin ƙasar nan da nufin samar da ababen buƙatu na zamani da ayyukan yi kusan 48,000 ga ƴan ƙasar.

Wannan matakin ya biyo bayan ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bai wa ƙanana da matsakaitan masana’antu damammakin tsayawa da ƙafafunsu don cike giɓin tattalin arziƙi da ake samu a fadin ƙasar.

Gwamnatin ta kuma raba tallafin N150,000 ga kananan ƴan kasuwa a jihar da nufin farfaɗo da jarin ƴan kasuwar.

Gwamnan jihar, Peter Mbah ya yi na’am da samun goyon bayan gwamnatin tarayyar, inda ya bayyana yadda shirin ya yi daidai da manufofin tsarin tattalin arziƙin jihar.

Shi ma shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Osita Ngwu, ya yaba da haɗin-gwiwar da ake samu a tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya a ɓangaren lura da fa’idojin samar da irin waɗannan cibiyoyi da ake samarwa ga jama’a.

Tun a farkon wannan shekarar ne Shettima ya ƙaddamar da irin waɗannan cibiyoyi a jihohi huɗu da suka hada da; Benue, Ogun, Ekiti, da kuma Jigawa.

By Babaji