Ku miƙa wuya yanzu ko a yi muku yadda aka yi wa jagororinku – Shugaba Tinubu ga ƴan ta’adda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi mayaƙan Boko Haram da ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da dukkan masu ayyuka makamantansu da ke haddasa rashin tsaro a Nijeriya su ƙaurace daga aikata harkokin ta’addanci ko kuma hukumomin tsaro su shafe su.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin wata lakca da ‘News Agency Nigeria’ (NAN) ta shirya a Abuja mai taken rashin tsaro a yankin Sahel daga shekarar 2008 zuwa 2024; ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta da tasirinsa acikin al’umma.

Shugaba Tinubu, wanda mai taimaka masa na musamman kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya wakilce shi, ya ce tsawon shekaru 15 kenan da ƙasar ke fuskantar taɓarɓarewar tsaro a ƙasar sakamakon mutanen banza na yin yadda su ke so.

Ya ce, lallai akwai buƙatar kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya inda acikin shekara ɗaya, an kashe aƙalla kwamandodin Boko Haram guda 300 yayin da ake ƙoƙarin daƙile ayyukan garkuwa da mutane.

Shugaban ya bayyana hakan a matsayin misali gare su kasancewar an kashe shugabanninsu da dama, ya na mai cewa matuƙar ba su miƙa wuya ba, to su ma hakan zai iya faruwa da su.

Ya ƙara da cewa, hukumomin tsaro na aiki kafaɗa-da-kafaɗa don ganin an magance matsalolin tsaro a ƙasar wanda hakan wani ɓangare ne na sabonta ƙasar kamar yadda ya ke acikin ajendar gwamnatinsa.

Sauran mahlarta taron sun haɗa da; Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa; Tsohon shugaban ƙasa, AbdulSalami Abubakar, Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, Idris Mohammed da sauran su.

By Babaji