Idan ka tsare gaskiya da riƙon amana, ba wanda ba za ka iya zama da shi ba – Usman Bala Muhammad
Daga NASIR S. GWANGWAZO
Za a iya cewa, ɗaya a cikin mutanen da suka yi sa’ar aiki a Nijeriya akwai Alhaji Usman Bala Muhammad, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin dukkan gwamnonin farar hula na Jihar Kano a Jamhuriya ta huɗu da muke ciki, kuma kowacce gwamnatin ta tafi da shi a mataki na ƙololuwa, musamman gwamnatoci biyu masu adawa da juna, wato na gwamnatin tsohon gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da gwamnati ta Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ba kasafai ake samun haka a siyasar Nijeriya ba. Kuma wani abin ƙarin birgewa shine, dukkansu ya yi aikin ne a maƙogwaron gwamnatocinsu. Bugu da ƙari, idan za a yi waiwayen baya, an san yadda siyasar ɓangaren tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, da ta tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau, ta zafafa, amma hakan bai hana dukkan gwamnatocin biyu tafiya da Alhaji Usman Bala ba. A taƙaice dai, babban abin lura shine, bayan Kwankwaso ya tafi a zangonsa na farko, Shekarau ya gaji Alhaji Usman Bala, haka nan Kwankwaso ya cigaba da tafiya da shi bayan ya dawo kujerar gwamna a karo na biyu, sannan Ganduje da ya gaje shi ya ɗora daga inda Kwankwaso ya bari, sai shi ma Gwamna Abba ya cigaba da tafiya da shi.
A tattaunarwarsa da Editan Blueprint Manhaja, NASIR S. GWANGWAZO, Alhaji Usman, ya bayyana sirrin wannan nasara tasa wadda ya tabbatar duk wanda zai riƙe shi, zai samu tagomashin da za a yi sha’awar aiki da shi a ko yaushe. Don haka idan kun shirya, sai mu ce, a sha karatu lafiya;
MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kanka.
USMAN: Sunana Usman Bala Muhammad, AMN. Ni ne mai ba wa gwamna shawara akan harkar aikin gwamnati na Jihar Kano, wato mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ko za ka iya gaya wa jama’a yadda aikin naka yake?
To idan aka ce mai bada shawara, kuma aka ce ga fagen da za ka bada shawara, a ce a harkar mulki, wato za ka iya duk wani abu da ya shafi aikin gudanarwarwa a harkar gwamnati. Ofishina na yana da ruwan da in ya ga akwai abinda zai inganta wannan yanayi, ya bada shawara. Ko kuma wasu ababe da suka je gaban mai girma gwamana, ake neman ya sahalince a yi su, sai kuma yake neman shawara kansu, zai iya turo min da wannan don in duba cancantar irin abinda aka turo, da kuma bada shawarar matsayin da ya kamata a ɗauka kai. Da kuma wakiltar mai girma gwamna a wasu taruka da ake buƙatarsa. Duk suna cikin ayyukan wannan ofis.
Shin gaskiya ne ayyukanka sun haɗa da duba ayyukan kwamishinoni ka duba kaga wanda ya kamata a yi?
A’a. Aikina da na kwamishinoni na da bambanci. Ai ni mai ba wa gwamana shawara ne. Su kuma suna ɓangaren zartarwa, wanda kowa abinda ya shafi ma’aikatarsa su suke gudanarwa, ko suke kai wa mai girma gwamna ya sahalance. Ni kuma duk abinda mai girma gwamna ya ga ya cancanta ya nemi shawara ta yana turo min, kuma zan bada shawara. Wanda ya shafi kowane ɓangare.
To an ga a baya ka yi gwamnatin da ta shuɗe ta jam’iyyar APC, a ƙarƙashin tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, har yanzu kuma kana cikin wannan gwamnati, kuma a maƙogaron ita wannan gwamnatin kamar yadda ka ke a waccan. Shin menene sirrin kasancewarka a gwamnatoci biyu duk da rashin jituwa da ke tsakaninsu?
To gaskiya zan iya cewa, babban jigo ga ma’aikaci, ko kuma in ce duk wanda yake ganin an ba shi wata amana, shi ne ya zama mai gaskiya, ya zama mai riƙon amana. Duk abinda za ka gaya wa shugaba, ka gaya masa abinda ya zama na gaskiya. Sannan idan ya ba ka amana, ka riƙe wannan amanar iya iyawarka. To koda ba a ɗauki abin nan da ka fada na gaskiya aka yi aiki da shi ba, nan gaba za a gano lallai abinda ka faɗa gaskiya ne, rashin ɗaukar abin kuskure ne.
To ma’aikacin gwamnati da duk ma abinda ka ke yi, ka kasance mai tsare gaskiya, mai bada shawara ta gari, mai kuma yin abinda ya dace. To duk wanda ya yi aiki da kai, zai yi sha’awar ya ci gaba da aiki da kai.
Ba wani abu ne na sirri ko na ban mamaki ba, na yi aiki a lokacin Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin kantoma, wato wanda ake kira kantoman riqo na ƙananan hukumomi. Na riƙe ƙaramar hukumar Warawa, sannan ina darakta na Ma’aikatar Muhalli ta jiha, na riƙe matsayin muƙadashi, kamar ‘acting permanent secretary’ na wancan lokacin. Da kwamishinan zai ta fi, shi ma ya yi handin oba, ƙarshe dai ni na riƙe Ma’aikatar Muhalli ta jihar a lokacin.
Da gwamnatin Shekarau ta wuce, Ina nan aka tura ni ofishin mataimakin gwamna a lokacin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin darakta na ayyuka na musamman. A lokacin mai girma gwamna Kwankwaso ne ke mulki.
Muka yi aiki har mai girma gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ga cancanta ta, ya naɗa ni babban sakatare na lokacin. Kuma ya bar ni a ofishin mataimakin gwamna, ni ne babban sakatare na ɓangaren mulki da sauran aikace-aikace. Saboda haka muka yi ta aiki da shi na kusanci, har lokacin da ya zama ɗan takarar gwamna, kuma aka zaɓe shi, bayan wa’adin mulkin Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ƙare.
To daga nan shi Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa ni matsayin shugaban fadar gidan gwamnati. Muka yi aiki da shi shekara ɗaya, daga nan ya canza min gurin aiki, na koma ‘permanent secretary’ a Ma’aikatar Lafiya. Bayan watanni aka turani, National institute for Policy and Strategic Studies’, wato makarantan nan ta Jos. Na je na yi karatuna ‘Senior Executive Course’, daga nan na zama mamba na wannan ‘institute’. Daga nan na dawo, aka sake mayar da ni ‘permanent secretary’ a Ma’aikatar Lafiya. Lokacin an yi zaɓe, babu kwamishinoni, muka riƙe ma’aikatar har zuwa ina ganin watan Disambar 2019. Sannan aka mayar da ni Ma’aikatar Yaɗa Labarai, wanda ina nan ne aka naɗa ni shugaban ma’aika na Jihar Kano.
Ina wannan matsayi na wasu lokuta, shi kuma shugaban fadar gwamnati, wato ‘Chief of Staff’ ya bar aiki don karan kansa, sannan mai girma gwamna ya sake cewa, ya naɗa ni in kula da wannan ofishin, na haɗa da nawa. Wanda waɗannan muƙaman guda biyu na riƙe har zuwa ƙarshen wa’adinsa.
To da yake ita kujera ta ‘chief of staff’ kujera ce ta siyasa gaba ɗayan ta. Don haka duk wa’adin waɗanda suke aiki a ƙarkashin mulkinsu ya ƙare, su ma wa’adinsu ya ƙare.
To da maigirma Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama zaɓaɓɓen gwamnan Kano, kuma aka rantsar da shi, wa’adin kujerar ya ƙare, amma na ci gaba da riƙe kujerata ta shugaban ma’aikata na Jihar Kano, har sai da na yi ra’ayin kaina, na ga ya kamata a ce na yi ritaya, duk da lokacin ritaya ta bai yi ba, Ina da sauran shekaru, amma na ga dacewar ya kamata in ajiye aiki, domin in ba wa wasu dama, su ma su riƙe. Wanda daga nan za a ga kowa irin rawar da ya taka.
To bayan na bari, mai girma gwamna ya ga shi yana sha’awar mu ci gaba da aiki da shi, wanda ya ce yana so mu ci gaba da aiki da shi. To ba mamaki ɗan zaman da muka yi da shi daga lokacin da ya karɓi mulki zuwa lokacin da na nemi yin ritaya ne ya fahimci wasu abubuwa da yake ganin yana son mu cigaba da aiki.
Kamar yadda na faɗa, duk wanda aka ce gaskiyarka ta ƙare, sai a ce waye shi, saidai a ce ƙaryarka ta ƙare.
Idan ka tsare gaskiya da riƙon amana, to ba wanda ba za ka iya zama da shi ba. Kuma ba wanda ba zai so ya yi aiki da kai ba. Amma idan ka zama marar gaskiya, marar amana, kuma ba ka yin aiki tuƙuru, to za ka zama ana gudun ka ko ana kyamar aiki da kai.
Wannan gaskiya abin sha’awa ne yadda ka iya aiki na kud-da-ƙud da tsohuwar gwamnati, kuma ka zo ka yi aiki a wannan. Amma wasu za su iya tunanin cewa, anya ba ko za a iya amfani da kai ba ne, wato a shirya wa tsohuwar gwamnati ƙulle-ƙulle?
(Dariya). To wannan hasashe ne, kuma kowa yana da irin nasa hasashen, amma me na ce maka, gaskiya na ce, duk wanda ya riƙe gaskiya ba ya buƙatar wani sharri, ba ka buƙatar ka cutar da wani, ko ka yi wa wani ado, ko ka ɓata shi. Duk abinda gwamnati ta yi ai a bayyane yake, idan ana son a san shi ai ba sai ta hannuna za a san shi ba. Shi aikin gwamnati na da ƙa’idoji, wannan ƙa’idojin da ake bi, da irin yadda ake adana bayanai na aikin gwamnati suna nan, duk abinda ake son a bincika za a samu, ko ina nan ko ba na nan. Ai shi ‘record’ shi yake bayanin abinda ya faru, ba shaidar wani ba, ko zancen wani ba.
Alhamdulillah. Mun gode sosai.
Ni ma na gode sosai.
