
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cire dangogin makamashi da suka haɗa da; gas na girki da na amfanin injina da motoci masu amfani da lantarki da makamantansu daga tsarin harajin VAT.
Daraktan hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Kuɗi, Mohammed Manga ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba inda ya ce Ministan Ma’aikatar, Wale Edun ya bayyana muhimman tsare-tsaren kuɗi guda biyu a ɓangaren gyara harkar mai da na gas.
Hakan na zuwa ne a wani yunƙuri na rage tsananin tsadar rayuwa ga al’umma da kuma inganta harkar mai a Nijeriya da Shugaba Tinubu ke yi.
Ministan ya kuma sanar da bada wani kaso na haraji ga ɓangare samar da mai da kuma gas kamar yadda doka ta tanadar.
Ya bayyana cewa, yin hakan wani ɓangare ne na shirye-shirye da Shugaba Tinubu ya samar na inganta ɓangarori daban-daban ga al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
