
Daga IBRAHIM HAMISU
Cibiyar fasahar sadarwa da ci-gaban al’umma ta (CITAD) ta ƙaddamar da rumbun yanar gizo tare da miƙa shi ga al’ummar ƙaramar hukumar Itas da ke Jihar Bauchi, a lahadin da ta gabata.
An gudanar da taron ne a harabar Hakimin gundumar Itas, inda ake sa ran tashar za ta samar da ingantaccen sabis na yanar gizo ga al’ummar yankin.
Yayin da ya ke jawabi, Malam Haruna Adamu Hadejia wanda shi ne babban jami’in da ke kula da samar da sabis ga al’umma na CITAD, ya ce, ita ce cibiya ta huɗu da CITAD ta kafa tare da tallafin Hello World.
Ya ƙara da cewa, manufar CITAD ita ce ta kafa irin waɗannan cibiyoyi guda 20 a dukkan shiyyoyin Najeriya guda shida don magance giɓin da ke akwai a harkar sadarwa.
Ya ƙara da cewa, yankin arewacin Najeriya ya koma baya a fannin sadarwa na zamani idan aka kwatanta da kudancin kasar, ya na mai cewa saboda haka ne yasa suka zo garin Itas aka gina musu wannan muhimmin rumbu don magance rashin daidaito a ɓangaren.
“A zamantakewa kuma akwai abinda ake cewa information age, ta yadda mutum zai zauna sai wanda ya je birnin Kano ne ya dawo ko wanda ya je Abuja ko Legas ya dawo shi ne zai baka labari. A’a, kana a ɗakinka za ka iya lalubo wasu labarai, to duk wadannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da muke so mutanenmu na karkara a dama da su.”
Mal.Gambo Idris
ya bayyana cewa, “a shekarar farko al’ummar wannan yanki za mu sha internet kyauta, bayan shekara ɗaya, idan za’a sabunta rijista za mu bada kashi 52% na kuɗin, yayin da CITAD za ta biya sauran kashi 48%.”
Ya kuma yi kira ga al’umma da su tabbatar da tsaro da ɗorewar rumbun, ta yadda za’a yi amfani da shi yadda ya kamata.
Blueprint manhaja ta ruwaito cewa wannan rumbu na ɗaya daga cikin babban shirin CITAD na daƙile bambancin da ke akwai tsakanin jama’ar karkara da na birane a Nigeriya.
