Tsaro: Yanzu kowa zai iya tafiya komai dare a Nijeriya – Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ikirarin cewa an samu ci-gaba ta fuskar tsaro a gwamnatinsa.

Tinubu, ta bakin mai ba shi shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu a yayin wata lakca da NAN ta shirya, ya faɗi hakan ne inda ya kamanta da yadda tsaro ya ke a shekarar 2022 da farkon 2023 a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na da kuma yanzu.

Ribaɗu ya ce daga yanzu, mutane za su iya tafiye-tafiye cikin aminci daga Abuja zuwa ko’ina a Nijeriya ba tare da fargaba ko tsoron riskar harin ƴan ta’adda ba.

Ya ce, a baya an yi ta samun hare-hare a wurare daban-daban ciki har da tashar jirgin ƙasa inda aka yi garkuwa da mutane da dama a shekarar 2022 da kuma fasa magarƙama da ƴan ta’adda suka yi tare da farmakar sojoji a Abuja.

Ya ƙara da cewa, yayin da ƴan bindiga suka buƙaci kuɗin fansa da adadinsa ya kai Naira biliyan 10.9, kaɗai abin da aka biya shine biliyan 1.05 cikin shekara guda wanda mafi yawancin jihohin da hakan ya shafa, daga arewacin Nijeriya su ke.

By Babaji