Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta yi gargaɗi ga wasu fitattun ‘yan Najeriya da suka haɗa da ‘ya’yan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf da Zahra, da su biya kuɗaɗen da ake bin su na filaye a cikin kwanaki 14, ko kuma su rasa haƙƙin mallakar su.
Ana sanar da duk wanda abin ya shafa cewa rashin biyan duk wasu kuɗaɗen filaye da kuma caji a cikin lokacin da aka ƙayyade zai haifar da janye tayin mallaka (R-of-O) akan filayen da aka ambata.
Hukumar da ke kula da babban birnin tarayya Abuja ta hannun hukumar raya babban birnin tarayya FCDA, ta yi barazanar janye haƙƙin mallakar filayen da fitattun ‘yan Najeriya suka mallaka idan har suka kasa biyan kuɗaɗensu cikin kwanaki 14.
Mutanen da abin ya shafa sun haɗa da:
– Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan shugaban ƙasa Bola Tinubu
– Abbas Tajudeen, kakakin Majalisar wakilai
– George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya
– Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan Harkokin Cikin Gida
– Bukola Saraki, tsohon shugaban Majalisar Dattawa
– Yakubu Dogara, tsohon kakakin Majalisar Wakilai
– Ovie Omo-Agege, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa
– Theodore Orji, Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun, tsoffin gwamnoni
– Dino Melaye, Kabiru Marafa, Stella Oduah, da Ben Bruce, tsaffin ‘yan majalisa
– Adamu Abdullahi, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa
– Ameh Ebute, Shugaban Majalisar Dattawan Jamhuriyya ta uku
