Tare da MUSTSPHA IBRAHIM ABDULLAHI
Gabatarwa
Istimna’i hanya ce da mace ko namiji ke bi, domin biya wa kansu buƙata ta sha’awa ta hanyar shafar zakari ko farji da hannu ko sandararrun abubuwa har sai su kawo.
Dabi’a ce mai illa ga lafiya sosai, amma kuma abin takaicin shi ne yadda kafofin intanet suka cika da bayanai akan alfanun yin istimna’i ba tare da mayar da hankali ga illolin da ya ke haifarwa a jiki ba.
A lokacin da na ce zan fara gabatar da rubutu akan wannan maudu’i, wani ya tambaye ni ko shin akwai alfanu a cikin yin zinar hannu tun da komai da ka sani yana da amfaninsa da kuma akasin haka? Sai na ba shi amsa da cewa, tabbas ya na da alfanu, amma fa matsalolin da yake haifarwa sun fi alfanun yawa. Kamar dai khamru uwar laifi, yadda Alƙurani ya gaya mana cewa, illolinta sun fi alfanunta yawa.
Wasu daga cikin amfanin yin istimna’i sun haɗar da: gamsar da kai, sauƙaƙe tsananin sha’awa, sannan wataƙila zai sa a samu bacci mai daɗi.
Bayan waɗannan, ni ban san amfaninsa a jiki ba. Abinda na damu shi ne, binciko matsalolinsa, domin sanar da alummata.
Illolin wannan ɗabi’a a jiki sun haɗar da illata tsarin tsokar naman jiki, hanyoyin zagayawar jini, ƙasusuwan jiki, jiyoyinjiki, fatar jiki (musamman fatar al’aura) da kuma cibiyar sarrafa jiki (ƙwaƙwalwa da laka).
Cikin yardar Allah, zan bi kowanne daki-daki na kawo bayanan illolinsa a rubutu mai zuwa, alabasshi daga baya na kawo muku hanyoyin da za a bi, domin dainawa da kuma abubuwan da za ku yi idan ya riga ya haifar muku da matsala. Mu tara a mako mai zuwa da yardar Allah.
Naku,
Mustapha Ibrahim Abdullahi
©MIAbdullahi 2024
