Atiku ya yaba wa mutanen Ribas da Fubara kan yadda suka bijire wa barazana

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yabawa mutanen Jihar Ribas da gwamna Similaye Fubara bisa jajircewa da kuma bijire wa tsangwama a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Atikun yayi wannan jawabin ne a shafin sada zumunta na X.

Ya bayyana gamsuwarsa da yanayin yadda aka gudanar da zaɓen. Yayi matuƙar farin ciki da kyara da tsangwama bai hana mutane fitowa su yi zaɓe ba.

Ya ƙara yabawa da irin jajircewa da mutanen Ribas su ka yi na ganin zalunci da siyasar uban gida bai yi tasiri ba.

Daga ƙarshe ya sake yabawa gwamna Fubara yadda ya gudanar da zaɓen cikin aminci duk da irin barazanar da aka samu lokacin zaɓen.

By ukarofi