
Daga BELLO A. BABAJI
An samu rahoton rasuwar Yariman Masarautar Zazzau kuma Ɗan-Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris bayan aukuwar wani hatsari akan hanyar Abuja-Kaduna da daren nan.
Kakakin Masarautar, Malam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Mamacin, mai shekaru 41, ya rayu ne da mata ɗaya da ƴaƴa biyu.
Kafin rasuwarsa, shi ne Mataimakin Sakataren Majalisar Masarautar.
A kwanakin baya ne mahaifiyarsa, Hajiya Habiba Shehu Idris, wacce ita ce mahaifiya ga Sarki na yanzu, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ta rasu.
Wakilin Blueprint ya ce iyalan mamacin za su sanar da lokacin da za a yi jana’izar sa.
