Gwamnatin Katsina za ta farfaɗo da kamfanin sarrafa fatu da ke garin Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina za ta farfaɗo da kamfanin sarrafa fatu da ke garin Daura a ƙaramar hukumar Daura.

Gwamna Dikko Raɗda ya sanar da haka a hira da manema labarai bayan ya kammala ziyarar gani da ido a Kamfanin wanda na ɗaya daga da cikin kamfanonin da tsohon gwamna a tsohuwar Jihar Kaduna marigayi Malam Balarabe Musa ya kafa a kananan hukumomi 14 shekara 42 da sauka wuce.

Mallam Dikko Raɗda ya nuna takaicin sa ganin shugabannin da su ka gabata ba su yi wani yunƙuri na farfaɗo da kamfanin ba.

Ya ce gwamnatin sa za ta tuntuɓi ma’aikatan ciniki da masana’antu domin duba yadda kamfanin zai fara aiki nan take da zarar an kammala aikin ginin kamfanin.

Haka kuma gwamnan ya umurci kwamishinan ƙasa da safayo da ya haɗa kan ƙwararru masana akan safaye na ma’aikatar su isa wurin aikin ginin kamfanin domin su gano duk abubuwan da ake buƙata na ci gaba da aikin ginin kamfanin.

Yace gwamnatin sa na ƙoƙarin haɗa kai da masu zuba jari na ciki da wajan ƙasan a kamfanin da zaran kamfanin ya fara aiki.

Malam Dikko Raɗɗa ya kuma sha alwashin duba yiwuwar farfaɗo da sauran kanfunan da tun lokacin marigayi Malam Balarabe Musa aka fara aikin ginin su amma akai watsi da aikin .

Ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na fito da hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin jihar.

By ukarofi