Jama’a sun ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Filato

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

Masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da zaɓe a Jihar Filato sun bayyana rashin jin daɗin su da yadda jama’a suka ƙaurace wa zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a dukkan faɗin jihar, a ranar Laraba 9 ga watan Oktoba, 2024, sakamakon rashin fita su kaɗa ƙuri’ar su ga ƴan takarar da suke so.

Wakilinmu da ya kewaya cikin garin Jos don ganin yadda zaɓen ke gudana, ya lura da yadda aka bar masu aikin zaɓe suke zaune suna gyangyaɗi babu masu zuwa zaɓe. Wata jami’ar zaɓe Juliana Jonah da ta yi aiki a wata cibiyar zaɓe da ke daura da Babban Masallacin Jumma’a na Jos ta ce, tun safe ƙarfe 8 da rabi suna wajen, don gudanar da aikin da aka basu, amma har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya da take ganawa da wakilinmu ko mutum ɗaya bai je kaɗa ƙuri’arsa ba.

Wani dattijo Baba Audu da ya gana da wakilinmu a Layin Zana cikin garin Jos, ya koka da halayyar da mutane suka nuna ta rashin fita wajen zaɓe a kan lokaci, duk da kasancewar an kai kayan aiki da ma’aikata da wuri.

Alhaji Ɗanlami Shu’aibu dake unguwar Abba Na Shehu ya nuna takaicinsa game rashin fitar jama’a wajen zaɓe wanda ya ce hakan na da illa sosai a sakamakon da za a samu, bayan kammala zaɓe.

Rahotanni daga sauran yankunan Jos da sassan Jihar Filato sun nuna lamarin duk iri ɗaya ne, jama’a ba su fita zaɓe sosai ba. Lamarin da wasu ke dangantawa da halin ƙuncin rayuwa na yunwa da talauci da ke addabar jama’a, da kuma sanin halin siyasar ƙasar nan, yadda duk Jam’iyya mai mulki a jiha ƴan takararta ne ke lashe akasarin zaɓen da ake gudanarwa, musamman a matakin Ƙananan hukumomi.

Sai dai duk da haka jama’a da dama sun yaba da yadda Hukumar Shirya Zaɓe ta Jihar Filato ta gudanar da zaɓen cikin tsari da lumana, yadda ba a samu wata tangarɗa mai yawa ba, bayan ta rashin buɗewar manhajar tantance masu zaɓe ta VVS da aka fuskanta, a farkon fara aikin zaɓen.

An gudanar da zaɓukan ne cikin ingantaccen tsaro da kwanciyar hankali, a dukkan ƙananan hukumomi 17 da ke jihar, wanda jam’iyyun siyasa 12 suka tsayar da ƴan takara a matakai daban-daban.

Shugaban hukumar zaɓe ta PLASIEC, Planji Chishak ya yabawa haɗin kai da haƙurin da jama’a suka nuna wajen gudanar da wannan zaɓe, duk da ƙalubalen kasa aikin manhajar tantance masu zaɓe ta VVS da hukumar ta ɓullo da ita, da ya haifar da tsaiko wajen fara zaɓen da wuri, wanda ya sanya hukumar ta ƙara wa’adin awoyi biyu, a kan lokacin da a baya ta ayyana rufe cibiyoyin zaɓe. Tun da farko dai hukumar PLASIEC ta sanar da cewa za a fara zaɓen ne da misalin ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 3 na yamma, amma tangarɗar sabuwar manhajar tantance masu zaɓe ya sa aka ƙara wa’adin.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta raba wa manema labarai a Jos, ta bayyana cewa, dokar zaɓen jihar a sashi na 119 ta amince idan an samu tangarɗar amfani da manhajar tantance masu zaɓe za a iya cigaba da tantancewa ta hanyar amfani da katin zaɓe na kai tsaye, domin kaucewa samun jinkiri da zai iya hana wasu amfani da ƴancinsu na zaɓen ƴan takarar da suke so.

An girke gamayyar haɗin gwiwar jami’an tsaro, domin sa’ido a kan zaɓen, musamman a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, inda take da tsohon tarihin rikice-rikice masu nasaba da siyasa.

Kamar yadda ba a raba ƴan siyasa da ƙorafi a lokacin zaɓuka, musamman idan sun ga wani yanayi da zai iya haifar musu da cikas wajen samun nasara, wani ɗan jam’iyyar LP Ebuka Zion ya yi zargin jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta shirya maguɗi ta hanyar amfani da ma’aikatan zaɓe na wucin gadi, waɗanda ƴan jam’iyyar PDP ne, cikin aikin zaɓen.

Jama’a da dama sun zargi PLASIEC da shirya ba daidai ba, wajen gaza fitar da sunayen mutanen da suka nemi shiga aikin zaɓe, bayan samun horo, a kan lokaci, kuma sunayen da aka fitar ba su yi daidai da na waɗanda suka shiga horarwar ba. Silas Pam da Fatima Aliyu da suka shiga aikin horar da masu aikin zaɓe a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, sun koka da yadda ba a fitar da sunayen akasarin waɗanda suka samu horo kan zaɓen da aka yi ba.

“Kwana uku muka yi ana ba mu horo, a GSS West of Mines, amma a ƙarshe sunayen wasu daban muka gani, da wasu tsiraru masu gata da aka zaɓa a cikinmu. Sannan sunayen da aka fitar awanni kaɗan kafin fara zaɓe bai fitar da asalin dukkan cibiyoyin zaɓen da ke wannan ƙaramar hukuma ba.” In ji Silas.

Ita kuwa Malama Fatima ta yi zargin rashin fitar da sunayen da wuri da cushen wasu sunayen na daban, alama ce ta akwai wata maƙarƙashiya da aka ƙulla da nufin yin maguɗi.

Isma’il Aliyu Entifa da ya tsaya takarar neman shugabancin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ƙarƙashin jam’iyyar ADC, bayan ya kaɗa ƙuri’arsa, ya ce suna kyautata zaton PLASIEC za ta kwatanta gaskiya kamar yadda ta yi musu alƙawari.

By ukarofi