Gwamnatin Katsina za ta samar da rumbunan sauƙi a ƙananan hukumomin jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A zaman Majalisar Zartarwa karo na goma ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa, ta amince da ƙirƙiro rumfar sauƙin.

Da ya ke hira da manema labarai jim-kaɗan bayan kammala taron majalisar, mai bai wa gwamna shawara kan ci-gaban karkara, Injiniya Yakubu Nuhu Ɗanja, ya ce gwamnatin da amince da haka ne domin sauƙaƙa wa al’umma duba da yanayi na matsi da ake fama shi.

Ya kuma ce, gwamnatin na duba yiwuwar faɗaɗa ƙirƙiro rumbun hatsi a kowacce mazaɓa 361 na jihar.

Injiniya Ɗanja ya ƙara da cewa, Gwamna Raɗɗa ya bada umurni da a ƙirƙiro rumfar guda biyu a ƙananan hukumomin da suke da manyan gari irin su Katsina, Funtua da Daura.

Taron majalisar zartarwa ya kuma amince da gyara masallatan Juma’a guda biyu a kowacce ƙaramar hukuma a jihar.

By Babaji