Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Hukumar National Inland Waterways Authority (NIWA) ta fitar da jerin dokokin da suka shafi sufuri a cikin jiragen ruwa da masu Kwale-kwale don rage yawaitar haɗurra a cikin ruwa da ke sanadiyyar hasarar rayuwa da milliyoyin nairori.
Hukumar ta NIWA a ƙarƙashin jagorancin Alh Abdulmalik Muhammad ta shirya wani gangamin wayar da kai a babbar kasuwar Yawuri don yaɗa sanarwa ga jama’ar gari da na karkara da suka zo cin kasuwa.
Kamar yadda shugaban hukumar Malam Abdulmalik ya bayyana, ƙa’idojin sun haɗa da amfani da rigar kariya, hana tashin jirage daga 6:00pm zuwa 6:00am, hana tashin jirage lokacin Iska, tabbatar da yin rajista na jirage ga NIWA, samar da kayan kashe gobara a cikin jirage, samar da filafilai da kuma gora ko kala da za a iya amfani da su idan inji ya samu wata babbar matsala, hana amfani da tsofaffin jirage da suka da kuma mugun lodi da ya saɓa hankali.
Hukumar dai ta fitar da wannan sanarwa ne saboda rage yawaitar haɗurran da jirage ke fuskanta mussaman in an saɓa ƙa’ida.
Wani direban jirgin ruwa da ke safara a yankin Yawuri ta jihar Kebbi zuwa jihar Neja mai suna Malam Umar Muhammad ya bayyana cewa ya samu sama da shekaru ashirin a cikin wannan sana’a amma bai taɓa ganin shekarar da ta zo da iftila’i irin ta bana ba saboda tun da ruwan ya zo da wuya a yi kwanaki goma ba tare da samun hatsarin da ke sanadiyyar mutuwa da hasarar dukiyoyi mai tarin yawa ba.
“Maganar gaskiya a nan ba za mu iya baiwa kowane fasinja rigar kariya ba kuma na tabbata gwamnati ba za ta iya ba, saboda misali yanzu jirgin da nake tuƙawa yana ɗaukar sama da mutane ɗari ta yaya zan iya bai wa kowane fasinja rigar kariya?
“Abin da za a yi dai shi ne a taƙaita yawan mutane da ya kamata kowane jirgi ya ɗauka amma dole ne sai hukumomi sun tsaya a tashoshin jiragen na ruwa.”
Bisa ga wata ƙididdiga dai masana sun nuna shekarar bana dai ita ce shekara mafi yawa da kuma munin haɗurra da aka taɓa samu a ruwan Yawuri da kuma Neja saboda tun farkon damina kawowa wannan lokacin da wuya a kwashe sati biyu ba ka ji an ce ko dai babban jirgin ruwa ko Kwale-kwale ko wata dabbar ruwa ta yi ɓarna ba.
