’Yan Nijeriya sun yaba wa Ahmad Musa da Shehu Abdullahi kan komawa Kano Pillars

Spread the love

’Yan Nijeriya, musamman ’yan arewa sun yaba wa matakin tsohon Kaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Ahmed Musa tare da Shehu Abdullahi, shi ma tsohon ɗan wasan na Super Eagles, na komawa buga wasa a Kano Pillars.

Karo na uku kenan da Ahmad Musa ke haskawa a gasar Firimiyar Nijeriya, inda a wasansa na farko da ya bugawa Pillars inda ya jefa duka ƙwallaye biyun da suka doke Sunshine Stars da su a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Wannan nasara da  Pillars ta samu, ta sanya ta kai wa matsayi na 7 da maki 7.

Ahmed Musa da Shehu Abdullahi dai na ci gaba da shan yabo kan komawa taka ledar da suka yi a gasar Firimiyar Nijeriya, matakin da da dama ake ganin ya kamata ya yawaita daga ‘yan wasan Nijeriya da suka yi fice a ƙasashen ƙetare.

Wannan ta sanya muhwara sake komawa sabuwa akan wasu daga cikin dalilan da suka sanya gasar ƙwallon ƙafar Nijeriya rashin cigaba, da kuma janyo ’yan wasa daga Turai zuwa gida kamar yadda ake so.

Daga cikin dalilan dai akwai ƙarancin ’yan kasuwa ko hamshaƙan attajiran da suke mallakar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, kamar yadda aka saba gani a ƙasashen Turai.

Saɓanin haka a Nijeriya akasarin ƙungiyoyin da ke haskawa a gasar Firimiyar ƙasar za ka mallakin gwamnatocin jihohi ne, waɗanda akasrin lokuta za ka kasafin kuɗin da ake ware musu takaitacce saboda dalillai da dama, waɗanda lokaci ba zai bari mu tattauna akai ba.

By ukarofi