Titin jirgin ƙasa na Kano-Maraɗi zai kammala a 2026 – Gwamnati

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Sufuri, Sanata Said Ahmed Alkali, ya bayyana cewa aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maradi wanda zai laƙume wa Nijeriya sama da Dala Biliyan 1.9 ana sa ran kammala aikin a watan Disambar 2026.

A cewar minstan, Gwamnatin Tarayya za ta biya kashi 15 na aikin yayin da kamfanin haɗin gwiwar zai samar da kashi 85 na kuɗaɗen matsayin rance wanda Gwamnatin Tarayya za ta biya a cikin shekaru 50 masu zuwa.

Ministan ya bayyana haka ne a ƙarshen makon da ya gabata yayin da yake duba aikin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Daura zuwa Maradi tare da wakilan kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sufurin ƙasa da suka kai ziyarar sa ido kan aikin.

Alƙali ya bayyana tsarin sufurin jiragen ƙasa na iya raba ɓangaren mai a matsayin wanda ya fi bayar da gudunmawar kuɗaɗen shiga na Nijeriya cikin ƙanƙanin lokaci.

Ministan ya ce tuni gwamnoni da dama ke zuba hannun jari a fannin sufurin jiragen ƙasa, daga Legas zuwa Filato, da ma na Kaduna, duk sun nuna sha’awarsu ta faɗaɗa layin dogo a jihohinsu.

Ya ce, “Manufar ɗaura ɗamarar ɓangaren shi ne a ba da damar shiga kamfanoni masu zaman kansu. Kazalika za ka ga irin ɗimbin jarin da gwamnatin tarayya ke yi a fannin don ganin an samar da ababen more rayuwa.

“A lokacin da za ku fara jigilar kayayyaki daga Legas zuwa Maradi, bisa ga yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta nahiyar Afirka, za mu samar da kuɗaɗe masu yawa, zai yi tasiri sosai ga tattalin arzikin ƙasar. A lokacin da muka haɗa tashoshin Fatakwal da Onne ta Aba zuwa Maiduguri, za ka ga sauyi za ka ga yadda za ta kasance kusa da mai.

A Jami’ar Sufuri ta Daura, Ministan ya bayyana shirin bai wa ɗalibai horo na musamman da zai sa su karɓe tsarin sufurin baki ɗaya.

Ministan ya kuma bayyana cewa an samu cigaba sosai daga ’yan kwangilar da ke tafiyar da aikin jirgin tun bayan ziyararsa ta ƙarshe.

“Na kuma umurci ɗan kwangilar da ya tabbatar da biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa a kan hanyar aikin,” inji shi.

A halin da ake ciki, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sufurin ƙasa, Sanata Adamu Aliero wanda ya jagoranci tawagar majalisar ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga aikin wanda ya ce zai yi matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasar. Ya ce a gaskiya kwamitin ya yaba da abin da yake gani amma akwai buƙatar a yi.

A cewarsa, ziyarar duba da yadda gwamnati mai ci ke ɗaura ɗamarar bai wa ‘yan Nijeriya sabuwar rayuwa.

Ya bayyana duk da haka cewa ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu ya fito ne daga kuɗaɗen takwarorinsu na gwamnatin Nijeriya domin kuwa daga sauran abokan hulɗar ba su zo ba.

A Jami’ar Sufuri ta Daura, Sanatan ya tabbatar da cewa an yi ayyuka da yawa don ganin an sanya jami’ar a matsayi mai kyau tare da jaddada cewa akwai buƙatar a yi.

“Jami’a ce ta kasa kuma domin ta samu damar ɗaukar ɗalibai daga ko ina a ƙasar, tana buƙatar fadada ayyukanta. Ya zuwa yanzu, da abin da muka gani, dole ne gwamnatin tarayya ta gina ƙarin kayan aiki.

A halin yanzu, kusan ɗalibai 1,300 ne kawai za ta iya karɓa daga cikin 5000, don shigar da su.”

By ukarofi