Daga RAHMA ABDULMAJID
A shekarar 2023 da ta gabata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Malam Nuhu muƙamin mai bai wa Nijeriya shawara kan harkokin tsaro wanda hakan ya zamo bambaraƙwai duba da cewa wadanda suka saba riƙe wannan kujerar kan fito ne da ga tsoffin manyan hafsoshin soji, yayin da shi kuma Malam Nuhu tsohon ɗan sanda ne. Hakan ya sa cikin wasu ƴan Nijeriya ya ɗuri ruwa inda suka riƙa dora alamar tambaya kan ko malamin zai iya kai bantensa..!
Ba kawai amsa wannan tambayar Ribaɗu ya yi ba, har ma da fito da sabon salo na iya riƙe sirrin ƙasa ya yi inda ya riƙa samun gagarumar nasara wajen magance matsalar rashin tsaron ba tare da ya bar siyasa ta kutsa ciki ba.
Malam Nuhu ya fara ne da tattara bayanai kan halin rashin tsaro da musababbinsa, tare da samar da wasu hanyoyi ciki har da buɗe kofar tuba, tuntuɓa, afuwa ga ƴan ta’addan da suka shirya ajiye makamai ga jami’an tsaro kamar yadda tsarin addini da gwamnati suka aminta.. Eh, Addinin Musulunci da Malam Nuhu ke bi ya ce “sulhu alkhairi ne”, haka ma Gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta son ganin Nijeriya na kashe ƴaƴanta da kanta, don haka bai wa uwa damar jiran ƴaƴanta su tuba su dawo kan hanya ba sabon abu bane a Nijeriya musamman ma idan uwar na cigaba da riƙon bulala na ganin yaran ba su cigaba da cutar da sauran ƴaƴan nata da sunan ba su damar tuba ba.
Shafi na biyu a dabarun Malamin shine murƙushe ta’addanci ba don neman suna ko arziƙi ba, sai don Nijeriya ta samu tsaro.
“Ba na son ‘Failure’, ban yarda na ɓata wuri a record ɗina ba.” Kalmomi ne ga duk wanda ya san Ribaɗu tun ya na shugaban EFCC ya ke furta su wanda hakan ya sa waɗanda suka san shi da zarar sun ji an ba shi wata ragama to fa sun san tsakanin sa da nasara babu shamaki sai dai kaddara!
Ku lura da wani abu a yaƙin Malamin da ta’addanci. Duk wanda Malamin ya ce an kashe daga ƴan ta’addar, to fa an kashe shi, saɓanin yadda a baya aka riƙa samun labarai masu karo da juna kan kashe ƴan ta’adda.
Misali, alƙaluma sun nuna cewa kusan sau shida ana kashe Abubakar Shekau a kafafen yaɗa labarai, amma can sai ka ji ya ɓulla. Fitattun nasarorin Malam a zuwa lokacin da nake rubutun nan sun haɗa da: – Ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, ciki har da ɗalibai 20 na bangaren kiwon lafiya – Ƴantar da wasu yankunan Katsina da Sokoto da Zamfara da Neja da Kaduna daga ƴan ta’adda – Kawar da jiga-jigan ƴan ta’adda irin su Halilu Sububu da Buhari Alhaji Halidu – Salwantar da sarakunan ɓarayi kamar su ɗangote, Boderi Isyaku, da Kachalla ɗan Chaki Dogo Gudali Dabarar da Malam Nuhu ke amfani da ita ta ɗauko asali ne daga ƙwarewarsa wajen iya tattara bayanai a matsayin ƙwararren ɗan sanda, kuma tsohon shugaban hukumar EFCC da ya taba yin ƙaurin suna wajen masu cin dunduniyar tattalin arziƙin kasa.
Haka ma amfani da dabarun shiga tsakani, da iya ƙulla yarjejeniyar kwance damarar kungiyoyin masu aikata laifuka. Komadai yayane, Malam Nuhu ya samu yabo daga gwamnonin jihohin da ke fama da ta’addanci da sauran al’ummar kasa. ƙwarewarsa a matsayinsa na shugaban EFCC na farko da kuma jami’in ƴan sanda ya ba shi damar tunkarar ƙalubalen tsaron ƙasa da duk iya ƙarfinsa.
Nasarar Malam Nuhu tamu ce, yi masa addu’ar nasara yi wa kai ne…
Rahma mataimakiya ta musamman ce ga Shugaban ƙasa kan Gidajen Rediyo a Ofishin Mataimakin Shugaban Nijeriya da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya
