Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya ziyarci iyalan ma’aikatan tsaron da suka rasa rayukan su a bakin aiki a lokacin da wasu ƴan ta’adda su kai musu kwantan ɓauna.
Sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi alƙawarin cigaba da kula da iyalan mamatan. Gwamnan ya yi wannan magana ne a lokacin da ziyarci fadar sarkin Tsafe .
Gwamnan ya bada tabbacin cewa irin wannan ba zai sa ke faruwa ba, sannan gwamnatin na duk abinda ya dace domin ganin ta kawo ƙarshen ta’addanci da ke addabar jihar.
Gwamnan daga ƙarshe ya bada gudunmuwar kayan abinci da kuɗaɗe ga iyalan mamatan.
Daga ƙarshe, sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa ya bayyana jin daɗin sa ga yadda gwamnan ya nuna kulawa da kuma jajircewa wajen ganin al’ummar Zamfara sun samu ingantaccen tsaro.

