Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A wannan mako ina so ne mu sake waiwayar batun tarbiyyar iyali, wanda ke ɗaya daga cikin muhimman abubuwan masu ɗaukar hankalin al’umma a wannan lokaci. Musamman idan mun lura da yadda ake samun ƙaruwar taɓarɓarewar tarbiyya a cikin al’umma.
Lallai babu shakka ina ganin akwai buƙatar iyaye su ƙara mayar da hankali wajen tarbiyyar yaransu da ke tasowa zuwa matakin samartaka ko ’yan matanci, waɗanda shekaru ne masu matuƙar haɗari a rayuwar yara, sakamakon yadda rashin jin su da ƙiriniyar su ke ƙaruwa. Har ma kuma su riƙa aikata wasu abubuwa masu haɗari a tarbiyyar su, waɗanda in ba a yi maganinsu da wuri ba, za su iya lalata makomar yaran bakiɗaya. Kamar halaye irin na shaye-shaye, sace-sace, da bin maza ko neman mata, ko bin lalatattun ƙawaye ko abokai.
Mun sani babu wani uba ko uwa da za su so lalacewar ɗan da suka haifa komai tsanani, sai dai in abin ya fi ƙarfinsu su miƙawa Allah lamarin. Duk kuwa da kasancewar akwai wasu iyayen da rashin sanin tarbiyya da sakaci ke sa wa su yi sanadin shigar yaransu cikin wani hali. Ko angiza su ga aikata wasu abubuwa da za su sa rayuwar su cikin haɗari, kamar su tallace -tallace, zuwa aikatau, ko tara samari don samun abin duniya, musamman ga ’ya’ya mata, waɗanda tarbiyyarsu ke da haɗari. Barin yara maza ba sana’a ko babu kyakkyawan ilimi, da kora su waje gun abokan da ba su da ingantacciyar tarbiyya shi ma haɗari ne sosai, da ka iya gurgunta musu rayuwa. Duk kuwa da salon maganar da ake cewa, komai ɗa namiji ya yi ado ne.
Na samu shiga wata muhawara da aka shirya game da wannan batu na fifita tarbiyyar ’ya mace kan ta namiji, da nuna ai komai ɗa namiji ya yi ado ne, wanda ya ja hankalin mutane da dama. Na nuna rashin amincewa ta da wannan tunani na wasu iyayen, domin kuwa kowanne ɗa Allah ya baka walau mace ko namiji duk amana ce, kuma za a tambaye mu ranar gobe ƙiyama game da yadda muka kula da amanar da Allah Ya ba mu. Kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki ya ke faɗa a Alƙur’ani mai girma cewa, dukkan mu masu kiwo ne, kuma za a tambaye mu kan abin da aka ba mu amanar kiwatawa.
To, wasu ba ma yara maza ne suke watsi da tarbiyyar su ba, har ma ’ya’ya mata, waɗanda nan gaba su za su zama iyayen al’umma. Mun sani ba kowanne uba ne ke sa ido kan ’ya’yansa mata ba, yana ganin wannan nauyin na kan uwar su ne, sai in akwai wata matsala sannan a sanar da shi. Ko mazan ma ba kowanne uba ne ke binciken yadda suke tafi da rayuwar su ba, bayan ba ya nan, don haka ake samun matsaloli a gida, ba da sanin uba ba, sai daga baya a yi ta jin kwaɓewar abubuwa, saboda an sakar wa uwa tarbiyya ita kaɗai. Ita kuma ta haɗe kai da ’yar ta sun zama ƙawaye, babu kwaɓa babu tsawatarwa. Wata uwar ma saboda rashin kula ba ta sanin halin da ’yar ta ke ciki, suna gida ɗaya har sai yarinya ta yi ciki ta zubar sau biyu ko sau uku, tana gaban uwar ta babu aure, amma uwar ba ta sani ba. Akwai labarin da na taɓa karantawa ma inda wata ’ya ta yi ciki har ta haihu a ɗaki uwar ba ta sani ba, sai da aka tsinci ɗan da ta haifa ta yar a kwararo, wasu suka tsinta.
Iyaye da yawa ba sa sanin halin da yaransu mata ke ciki, ko don rashin mayar da hankali a kansu, ko don rashin sauraron matsalolinsu da iya ba su tallafin da suke buƙata don kula da rayuwar su. Ko rashin damuwa da abin da suke yi a ɗaki su da ƙawayensu ko in sun fita wajen samarin su. Rashin sanin waɗannan abubuwa na sa yarinya ta riƙa aikata abin da ta ga dama, ko ta riƙa ɗaukar shawarar da ƙawayenta suke bata ko abin da ta ga suna yi. Ko ma dai ta riƙa kwatanta abin da samarinta ke aikatawa kamar shaye-shaye ko shiga harkar daba. Muna ganin irin waɗannan yara da suke samun kansu a halaye na rashin tarbiyya, ba a son ransu ba, sai don ba su samu iyaye nagari ba, ko sun tashi a cikin wata gurɓatacciyar anguwa, da mazauna cikinta ba su da tarbiyya mai kyau, ko kuma ana aikata abubuwan assha da yawa a kewayenta.
A cikin matakan tarbiyya da shawarwarin da masana ilimin zamantakewa ke bayarwa, akwai batun zama a muhallin da zai dace da tarbiyyar da ka ke so ka bai wa yaranka, baya ga zaɓa musu iyaye nagari masu cikakkiyar tarbiyya. Talauci na taka muhimmiyar rawa wajen lalata tarbiyya, saboda idan mutum ba shi da ƙarfin da zai iya kama haya a irin unguwar da yake buƙata don makomar rayuwar yaransa ba. Ko samun auren wacce ta dace da tarbiyyar da yake son bai wa yaransa ba. Sai dai ba shi ne ke tantance mai tarbiyya da rashin tarbiyya ba, ana samun masu halayen ƙwarai da tsoron Allah daga cikin talakawa, ana kuma samu daga gidajen masu kuɗi ko masu sarauta. Haka lalacewar tarbiyya ita ma ana samu daga kowanne ɓangare.
Samun maƙwafta nagari masu riƙo da addini, da za su kare tarbiyyar iyalinka kuma ba za su keta haddin iyalanka ba, abu ne mai matuƙar muhimmanci sosai. Ba na mantawa akwai wani rahoto da na taɓa aiki akai game da yadda wasu maƙwafta suka riƙa lalata da yaran maƙwafcin su. Yayin da aka zargi wani daga cikinsu yana wasannin da ba su kamata ba da ƙananan yaran da ba su kai munzalin balaga ba. Wannan abu ya faru da yara mata bakwai ’ya’yan mutum ɗaya, ko da yake ba a lokaci guda ba, amma a zantawar da na yi da su sun ce duk lokacin da abin ya faru suna sanar da iyayensu, amma uban ba ya iya ɗaukar wani mataki, saboda tsoron lalacewar zumunci tsakanin sa da makwafcinsa. Har sai lokacin da ɗaya daga cikin matan mutumin da ake cin zarafin ’ya’yan su ta kasa haƙuri ta fallasa abin da ke faruwa, hukumomi da ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin mata suka shiga batun. Zama a tsakanin gurbatattun mutane matsala ce mai girma ga tarbiyyar iyali.
Yadda wasu ke riƙon sakainar kashi da al’amarin tarbiyyar ’ya’yansu abin takaici ne sosai. ’Ya’ya mata rahama ne, kuma suna zama sanadin tsira da ceto ga iyayen da suka kula da tarbiyyar su har zuwa auren su. Mata su ne iyayen al’umma, domin kuwa su ne masu ɗaukar ciki da haihuwa da raino, da kuma uwa uba tarbiyyar yara. Haka kuma namiji a matsayin sa na jagoran gida, mai hidimar iyali da ɗaukar ɗawainiyar gida, da kula da ’yan uwansa, har ma da iyaye idan sun girma. Kuskure ne a riƙa fifita tarbiyyar wani daga cikin yara, namiji ko mace, domin kowannen su da irin nauyin da ke kansa da hikimar halittar sa.
Babu mamaki irin yadda masana tarbiyya ke ganin ƙalubalen da ake fuskanta a mafi yawan gidajen aure ta yadda ake samun nutsattsun yara mata, da kangararrun yara maza. Kuma daga cikin waɗannan yara mazan ne za su auri irin yara matan da muka killace muka ba su muhimmanci da tarbiyya tagari. Idan aka samu mata mai tarbiyya da miji marar tarbiyya, zamantakewar aure tana samun babban ƙalubale da rashin jituwa, da tauye haƙƙi, saboda kowanne ya taso cikin wata tarbiyya ta daban. Shin kana ganin ya dace ka aura wa ’yar ka irin ɗan da ka wofintar da tarbiyyarsa?
Lallai iyaye su fahimta cewa, ’ya’ya dukkan su albarka ce daga Ubangiji, kuma nauyi ne babba a kan mu, mu ba su kyakkyawar tarbiyya, ilimi mai inganci, da tsoron Allah. Mu yi wa yaran mu tarbiyya yadda za su tashi su zama abin alfahari ga kowa, su zama irin surukan da za mu yi burin samu, irin maƙwaftan da za mu yi kwaɗayin zama kusa da su, saboda kyawun halayensu da kyakkyawar tarbiyyar da suka samu.
Mu ɗora yaran mu maza kan tarbiyyar da za su zama mazajen aure nagari, iyaye abin alfahari, kuma shugabannin gobe masu adalci da tsoron Allah. Mu bai wa yaranmu mata tarbiyyar da za su taso su zama abin alfahari, abin sha’awa ga kowa, matan aure nagari, iyaye nagari, masu hangen nesa da tallafawa mazajen su wajen gina al’umma mai cike da ƙauna, tausayi da tsoron Allah.
