‘Yan sanda sun kama nakasassu uku a yayin ƙwace adaidata sahu a Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴan sanda a Jihar Legas, sun kama wasu nakasassu uku da suka yi yunƙurin ƙwace wani adaidata sahu a yankin Okobaba da ke garin Ebute-Meta.

Mutane ukun sune; Mande Bello mai shekaru 30 da Samsudeen Usman mai shekaru 23, sai kuma Gazali da ba a san adadin shekarunsa ba waɗanda rahotanni suka bayyana cewa ƙwararru ne su a harakar ƙwacen adaidata.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kama ɓarayin wa jaridar Blueprint inda ya ce mai adaidatan shi ya kai kara ga babban ofishin rundunar da ke Denton.

SP Hundeyin ya ce mai adaidatan ya rage wa ɓarayin hanya ne daga Shataletalen Boson Oyingbo inda suka nemi ya sauke su a yankin gadar Third Mainland wanda da farko ya ƙi amincewa da hakan.

A lokacin da mai adaidatan ya yi yunƙurin sauƙe su ne sai Mande ya fitar da wa kebul inda suka fafafa da shi har ta gai Garzali ya gudu inda ya juyo da sauran biyun zuwa Okobaba waɗanda a nan ne ƴan sandan suka kama su.

By Babaji