Me ke kawo furfura

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Canzawar lauyin gashi daga baƙi zuwa fari, wata al’ada ce ta ɗan adam, duk da cewa, ana alaƙantata da tsufa kawai, sai dai akwai ababe da yawa da ke iya kawo furfura baya ga tsufa.

 Shafin kwalliya na wannan mako zai tattauna kan asalin dalilin samuwar furfura a gashin jiki.

A lokacin da ƙwayoyin halittar ɗan adam suka yi ƙasa, ma’ana tsufa ya fara zuwa masa, ƙofofin gashi na jiki da suke haifar da sinadarin ‘melanin'(melanin wani baƙin abu ne da yake tsiro a mahudar gashin mutum wanda yake sa fata ta canza launi.)

Raguwar wannan sinadarin da ke ba wa gashinmu lauyin baƙi ne zai sa gashi ya fara fita ba tare da kala ba. Wannan ne sananniyar mafarin furfura, wadda hakan kan faru ne kawai a lokacin da ka fara manyanta. 

Wasu masana sun ce, furfura ba tana nufin gashin ka ne na asali kafin haɗuwa da sinadarin melanin ba, kamar yadda wasu ke gani. Furfura yanayi ne da ke samun jikin ɗan adam a ƙoƙarin bayyana wani canji da jikin ke ciki. Wasu kuwa sun fassarata da cewa, sinadarin melanin idan ya raunana ne yake koɗewa, daga baƙi ya fara fitar da fari-fari wanda zai haɗe da ainahin kalar gashi a lokacin tsirowarsa wanda shima ba fari ƙal ba ne. haɗuwr waɗannan kalolin ne za su ba da farin gashi ko ince furfura.

Idan za mu lura da kyau, a lokacin fara fitowar furfura, ba ta cika haske sosai ba kamar ta wanda ya jima da ita ba, dalili, kai da kake farkon fara farin gashi, kana da ragowar ƙwayoyin hallitar da ke haifar da sinadarin melanin, don haka yana ƙoƙarin fitar da ɗan ragowar abin da zai iya fitarwa daga launin baƙi, duk da cewa ba mai wani ƙarfi ba ne, don haka gashin sai ya fara da launin ruwan ƙasa, har a kai ga sinadarin ya koma fitar da launin fari a ƙoƙarinsa na yin aikin da ya saba, wanda zai haɗe da ainahin kalar gashi su bada kalar furfura.

A wani ɓangare kuma za a iya haɗuwa da furfura ko da tsufa bai zo ba, kamar yadda na faɗa a baya, ɗaya daga cikin ababen da ka iya kawo furfura a lokacin ƙurciya akwai wasu daga cikin rashin lafiya. Misali; cutar ‘thyroid’ da kuma cutuka da suka faɗa a irin rukuninta, wato masu taɓa gaɓoɓin da ke ɗauke da sinadarin da ke taimakon jiki a yayin girma wato hormone, wanda tasirinsa ga aikace-aikacen ƙwayoyin halitta da matattararsu mai yawa ce. Idan hakan ta kasance, cutar za ta iya taɓa ƙwayar halitar da ke kula da sinadarin melanin, hakan zai iya kawo furfura ko da ba a kai shekarun yin ta ba.

Hakazalika damuwa da kuma rashin samun hutu hanyoyi ne masu kai gashi ga furfura kamar yadda masana suka bayyana, domin dukkansu na iya kawo rauni ga melanin, wanda zai hana shi haifar baƙi ga gashi kamar yadda ya saba.

Wasu malamai sun ce, yawan kusantar iyali na ɗaya daga cikin ababen da ka iya haifar da furfura. A bayanin na su, wannan ya faɗa ne kan jinsin mutanen da ake kira Harijai, ma’ana, masu yawan sha’awa. To idan kusantar ta yawaita sosai, za a iya samun farin gashi.

Harwayau, furfura za ta iya zama gado, ma’ana, idan mahaifi ko mahaifiyarka ta yi furfura da wuri, akwai yiwar ka gaje ta. Wannan na nufin ko babu dalilai na sama za a iya samunta a matsayin gado. 

Ta wani ɓangaren, ƙarancin sinadarin bitamin B kan iya zama silar fitowar farin gashi, domin rashinsa na iya raunana fitowar melanin yadda ya kamata, wanda hakan ka iya sa furfura samun matsuguni. Duk da cewa, wannan bai cika zama matsala babba a wannan ɓangare ba, domin sai ya yawaita ne zai kawo hakan. Tasirinsa bai kai na damuwa da rashin ba wa jiki abin da yake buƙata na daga abinci ba

By ukarofi