Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar hana sha da fatauci ƙwayoyi NDLEA ta kama wani mutum ɗauke da hodar ibilis mai nauyin 0.642 a kan hanyar Kano zuwa Kankia.
Kwamandan hukumar a Katsina Muhammad Aminu Abubakar ya bayyana wa manema labarai haka a ofishin hukumar.
Ya ce wanda ake zargi da aikata laifin, ya faɗawa jami’an hukumar cewa yana kan hanyar sa ta zuwa jamhuriyar Nijar.
Kwamandan ya ƙara da cewa hukumar na nan na faɗaɗa bincike akan mai laifin da zaran an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ya yi gargaɗi cewa zai yi amfani da duk dokokin da hukumar ta tanadar wajan yaƙar masu safara da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.
Ya kuma yi alƙawarin haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki domin yaƙar wannan mummunar sana’a.
Kwamandan wanda yau mako biyu kenan da isowar sa Katsina ya canji tsohon kwamanda Hassan sani da aka mayar hedikwatar hukumar.
