Gwamna Lawal ya ba ƙungiyar tsoffin sakatarorin dindindin na Zamfara motar bas

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya sanar da cewa Gwamna Dauda Lawal ya ba da gudunmawar motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 ga Ƙungiyar tsoffin sakatarorin dindindin na Zamfara.

Idris ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce gwamnan ya cika alƙawarin da ya yi wa ƙungiyar a taron shekara-shekara na bara. A cewar sa, an miƙa motar ga shugabannin ƙungiyar a fadar gwamnati da ke Gusau.

Ya ƙara da cewa, “Tun a taron bara, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin samar wa ƙungiyar motar da za ta taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga yayin ayyukan su. Yau, Alhamdulillah, gwamnan ya cika wannan alƙawari.”

Gwamna Lawal ya ce, “Ina roƙon Allah ya sa ku amfana da wannan mota a ayyukan ku na yau da kullum. Gwamnatina za ta ci gaba da ba ku duk goyon bayan da ya dace, domin kun yi wa Jihar Zamfara hidima da ƙwazo. Yanzu lokaci ya yi da gwamnati za ta nuna goyon baya ga ƙungiyar ku.”

A yayin karɓar motar a madadin ƙungiyar, tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Karakkai, ya bayyana farin cikin ƙungiyar da wannan tallafi na gwamnati. Ya ce, “Wannan shi ne karo na farko da gwamna ya nuna kulawa da ƙungiyar mu tun bayan ƙirƙirar jihar. Muna godiya ga Gwamna Lawal saboda cika alƙawarin da ya yi. Allah ya saka masa da alheri.”

By ukarofi