
Daga BELLO A. BABAJI
Tawagar ƙungiyar finafinan Afirka da na yarukan Kano da bukukuwansu (KILAF) ta karɓi baƙoncin wakilan Gidan Buɗe Ido na Ƙasa (NGA) don tattauana batutuwan haɗin-gwiwar da suka alƙanta su.
Cikin wata sanarwa da shugaban KILAF, Mista Abdulkareem Mohammed ya fitar, ya ce tattaunawar ta cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu wanda ya gudana ne la’akari da gagarumin taron KILAF da za a yi a daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2024 a Kano.
Shugaban ya ce kawo yanzu KILAF da NGA sum cimma matsayar inganta harkokin al’adu da wasu sana’o’in hannu da al’umma suka dogara da su.
Aƙalla ƙasashe 66 ne za su bajekolin al’adunsu a yayin taron wanda za a yi a Ado Bayero Mall da ke Kano inda za a ɗauki tsawon kwanaki biyar ana yi.
Wannan dai wata alama ce da ke nuna cewa KILAF na samun cigaba ta fuskar ayyukanta da ma inganta harkokin al’adu a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya.
