Yadda shari’a ta zama wasan kwaikwayo bayan rashin sanin inda wanda aka tsare ya ke

Spread the love

DAGA BELLO A. BABAJI

An samu wani abin mamaki a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan da aka nemi babban ma’aikacin kamfanin Binance Holding Limited, Tigran Gambaryan ba a gan shi ba bayan an tsare shi na zaman dakon shari’a wadda aka shirya yi a yau Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Shari’a Emeka Nwite na kotun ya ayyana ranar 18 ga watan Oktoba don gurfanar da kamfanin da ma’aikacin kan badaƙalar wasu kuɗaɗe da hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta shigar.

A lokacin da aka shirya tsaf don sauraren ƙarar ne, sai aka nemi Gambaryan aka rasa wanda hakan ta sa Alƙali Nwite ya tambayi lauyan da ke kare shi kan ina ya ke, inda ya amsa masa da cewa shi ma bai san inda ya ke ba.

Baya ga haka ne, sai Alƙalin ya nemi ji daga wani jami’in Hukumar Gyaran Hali (NCoS) game da inda Gambaryan ya ke, sai ya amsa masa da cewa ya san an kawo shi wajensu, amma a halin da ake ciki bai san ina ya ke ba. A nan ne ya umarce shi da ya binciki kurkukun Kuje inda a nan aka tsare shi don samo cikakken bayani game da lamarin.

Daga bisani, an gano cewa Gambaryan bai halarci kotun ba ne sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita, inda lauyansa ya buƙaci kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa wani lokaci.

By Babaji