Shettima ya buƙaci ƴan kasuwa su yi amfani da damar kasuwancin zamani don bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga manyan ƴan kasuwa da su ya amfani da damammaki wajen zuba hannun-jari a ɓangarorin daban-daban don bunƙasa harkar tattali a Nijeriya.

Ya ce akwai buƙatar a sanya hannu a ƙananan masana’antu, noma, harkar tattali na zamani, ingantayya da makamantansu.

Wata takarda daga Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harakokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha, ta ce harkar zuba hannun-jari na ƙasashen waje da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tsara, ya samu ƙaruwa a ranar Alhamis bayan da ƴan kasuwa da dama daga ƙasar Sweden suka ƙudiri aniyar zuba miliyoyin daloli a harkar tattali, lafiya and wasu manyan ɓangarori a Nijeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da Shettima ya bai wa ƴan kasuwar tabbacin samun tagomashin da ke tattare da ci-gaba da ake samu a ɓangaren bunƙasar kasuwanci da tattali a ƙasar a ziyara da ya kai wa ƴan ƙasar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce, gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauki matakan da suka dace wajen ganin ta daidaita al’amuran harkokin tattali tare da mayar da hankali kan tsara kasuwancin da ƴan kasuwa na gida da na waje da su yi burin zuba hannayen jari a ciki.

By Babaji