Zanga-zanga: Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen mutum 76 da za ta gurfanar gaban kotu

Spread the love

An kama masu zanga-zanga guda 76 a Abuja, Kaduna, Gombe, Jos, Katsina, da Kano, yayin zanga-zangar da aka gudanar daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta, 2024, a sassa daban-daban na ƙasar.

Zanga-zangar ta samo asali ne daga matsalar tattalin arziki mai tsanani, wanda ya sa ‘yan Najeriya da dama suka hau tituna don nuna damuwarsu.

A wannan lokacin, an ruwaito cewa jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa, sun kama wasu, kuma a wasu lokuta sun harbi masu zanga-zangar.

A cikin wata tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CS/503/2024, mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Satumba, kuma da wakilinmu ya gani ranar Juma’a, masu zanga-zangar da ke fuskantar tuhumomi 10 na nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya da aikata laifin cin amanar ƙasa.

Daga cikin masu zanga-zangar 76, 32 yara ƙanana ne daga shekara 14 zuwa 17.

An lissafa masu zanga-zangar da aka kama daga na 1 zuwa na 76 a cikin takardar tuhuma; Nura Ibrahim 24, Abdulbasi Abdusalami, 34, Ahmed Yusuf 25, Awolu Abdulahi 21, Umar Musa 15, Muhammadu Mustapha 16, Umar Muhammed 23y, Umar Inusa 18, Abdullahi Sani 21, Abba Usman 30, Ibrahim Rabiu 16, Abubakar San, 19, Abubakar Abdullahi 18, Amir Muhammed 17yrs, Umar Ali 17, Saminu SANI 22, Muhammed Musa 14, Suleiman Dauda 18, Ismail Abdullah 27 da Haruna Suleiman 22.

Sauran sun haɗa da: Bello Abdullahi 23, Usman Yunusa 20, Umar UMAR 25, Sani Aliyu 17, Yusuf Lawal 21, Abba Adamu 22, Abbas Hamza 20, Tasiu Lawal 16, Jamilu Haruna 16, Usman MOHAMMED 20, Aminu Usaini 20, Aminu Mohammed 24, Abdullahi Suleiman 16, Bilal Auwalu 15, Umar Kabir 22, Abubakar Ibrahim 18, Usman Yusuf 22, Abubakar ADAM 16, Suleiman Ali 16, Mubarak Hamza 23, Ibrahim Musa 24, Samani ALI 25, Yahaya Sani 20, Umar Sani 26, Abbas Haliru 24, Sani Idris 17, Tashiru Mohammed 18, Abdulaziz Abubakar 15, Usman Sirajo 16 da Musa Adam.

Sauran sune; Mukhtari Yahaya 17, Abba Ahmad 23, Umar Mohammed 24, Yahaya Musa 18, Umar Abdullahi 17, Salisu Adamu 16, Habibu Sani 17, Sadiq Sanusi 15, Ibrahim Sani 17, Mustapha Kabir 16, Saifullah Mohammed 17, Hassan Mohammed 17, Mustapha Abubakar 17, SANUSI Nura 14, Abdulmalik Auwal 19, Musa Ishaku 17, Abdulrahman Ibrahim 17, Usman Ibrahim, Usman Fatihu 21, Abdulganiu Musa 15, Sagir Hassan 19, Saidu Usman 25, Abubakar Muhammed 22, Kabiru Sani 25, Muhammed Yahaya 14, Mukhtar Alhassan 16, da Mustapha Ibrahim 18.

A cikin tuhume-tuhumen da Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya shigar ta hannun lauyansa, Simon Lough, masu zanga-zangar da wasu da ba a kama ba an tuhume su da abubuwa kamar haka:

Tuhumar farko ta ce, “Daga ranar 31 ga Yuli 2024 zuwa ranar 4 ga Agusta, 2024, a Abuja FCT da Kano, cikin hurumin wannan kotu, kun yi ƙoƙarin tayar da zaune tsaye a Najeriya tare da cin amanar ƙasa.

Gwamnati ta lura cewa masu zanga-zangar sun aikata laifi da ya saɓawa sashi na 96 kuma da hukuncin ƙarƙashin sashi na 97 na Kundin Tsarin Laifuffuka.

Tuhumar ta biyu ta ce, “A cikin hurumin wannan kotu kun yi yunƙurin wato: ƙoƙarin tayar da tarzoma, kuma ta haka sun aikata laifi da ya saɓawa sashi na 96 da hukuncin ƙarƙashin sashi na 97 na Kundin Tsarin Laifuffuka.”

Tuhumar ta uku ta ce, “Daga ranar 31 ga Yuli 2024 zuwa 10 ga Agusta, 2024, a Abuja FCT, Kaduna, Kano da Gombe, cikin hurumin wannan kotu, an kama ku tare da Andrew Martin Wynne (wanda aka fi sani da Andrew Povich), ɗan ƙasar Birtaniya, da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta kuma zarge su da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya ta hanyar kira ga soja su karɓi gwamnati daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sannan an tuhume su da ɗaukar tutar Rasha da rera waƙoƙin tashin hankali ba tare da izini ba da kuma ɓarnata ofisoshin NCC.

A ranar 2 ga Satumba, Egbetokun ya gurfanar da masu zanga-zangar #EndBadGovernance guda 10 a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya bada su beli akan tsabar kuɗi miliyan N100.

Duk da haka, wasu guda 5 sun kasa cika sharuɗɗan belin, wanda ya sa suka shigar da buƙatar sassauta sharuddan, kuma Mai Shari’a Nwite ya amince da rage belin zuwa miliyan N5 kowanne daga cikinsu.

By ukarofi