Wata mata ’yar ƙasar Indiya ta kai ƙarar mijinta kwanaki 40 kacal da aurensu, inda ta yi ikirarin cewa sau ɗaya ko sau biyu kaɗai yake wanka a wata.
Matar da ba a bayyana sunanta ba daga Agra, a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, ta je cibiyar ba da shawara ga iyali don yin ƙorafi game da rashin tsaftar mijinta, inda ta bayyana cewa ba kasafai mijin yake yin wanka ba, yana saka tufafi mai datti, kuma yana warin baki.
Ta ƙara da cewa, da kyar take iya tsayawa kusa da mijin, ballantana ta haɗa jiki da shi.
Sakamakon haka, bayan kwana 40 da yin aure, ta nemi a raba auren.
Lokacin da cibiyar ba da shawara ta tambayi mijin, mai suna Rajash, ya yarda yana wanka sau ɗaya ko sau biyu a wata kuma yana tsaftace jikin ne ta hanyar yayyafa ruwa a jikinsa da Gangajal (ruwa mai tsarki daga kogin Ganges) sau ɗaya a mako.
ɗaya daga cikin masu ba da shawara a cibiyar iyali da ke Agra ta shaida wa manema labarai cewa, sababbin ma’auratan sun fara samun sa-in-sa game da tsaftar mijin makonni kaɗan bayan ɗaurin aurensu.
Daga ƙarshe, matar ta bar gidan, ta koma zama da danginta. Ba da daɗewa ba, danginta suka shigar da ƙara a ofishin ’yan sanda da ke yankin tare da neman a raba aurensu.
Matar ta ce, Rajash ya yi wanka sau 6 a cikin kwanaki 40 da suka gabata, wanda ya fi yadda ya saba yi, saboda ta dage. Jin labarin yanke shawarar rabuwa da shi, mijin ya yi alƙawarin yin tsafta har ma da yin wanka a kullum, amma dangin matar sun ce ba ta son yin sulhu da shi.
