Rundunar ’yan sandan jihar Legas a ranar Lahadi ta tabbatar da cewa wani mutum ya yi tsalle ya faɗa kogi sakamakon shan miyagun ƙwayoyi mai suna Colorado.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ’yan sandan, O. Hundeyin, ya raba wa manema labarai a jihar Legas.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 11 na safe, inda ya ƙara da cewa, an samu rahoton koke a sashin Alagbado cewa wani Kazeem mai shekaru 45 a duniya da ya yi ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da ake kyautata zaton Colorado ne ya yi tsalle ya faɗa kogin da ke kan iyaka tsakanin Legas da jihar Ogun.
“Bayan haka, wanda ain ya shafa ya nutse a cikin kogin kuma ya mutu,” inji shi.
“Nan da nan jami’an ’yan sanda na sashen suka ziyarci wurin, sannan aka ɗauki hotunan marigayin, kuma da aka tuntubi mahaifinsa ta wayar tarho ya ba da umarnin a binne gawar nan take a gefen kogi, kamar yadda al’adarsu ta tanada,” inji Hundeyin.
Sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan bayanan da ke da alaƙa da mutuwarsa.
