Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dokokin Nijeriya, ya bayyana damuwarsa kan tsadar man fetur, abinci, da kayan masarufi, wanda a cewarsa yana galabaita ‘yan Nijeriya.
A cewar Ndume, ’yan Nijeriya da dama ne ke shan wahala saboda tashin farashin kayayyakin masarufi.
Ndume ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya kuma ce ci gaba da ƙara farashin man fetur da abinci da kuma kayan amfani na yau da kullum na ƙara jefa ’yan Nijeriya cikin ƙunci da wahala, musamman ma talakawa.
Tsohon mai tsawatarwa na majalisar ya ce wasu ɓata-gari cikin gwamnati na ƙoƙarin haddasa fitina tsakanin mutane da gwamnatin Tinubu ta hanyar ɓullo da tsare-tsare masu tsauri da kuma mara kyau maimakon shawo kan matsalar hauhawar farashi da kuma tashin kuɗin dala da ke ci gaba da kassara ’yan ƙasar.
“Wasu ne kawai ke son ɓata Tinubu a idon jama’a ta hanyar ɓullo da waɗannan tsare-tsare daga karshe kuma laifi ya koma kan shugaban.
“Ina kira ga shugaban ƙasa da ya daina kula waɗannan mutane da ke son kawo cikas ga gwamnatinsa. Halin ƙunci da mutanen ke sa ‘yan Nijeriya ba zai misaltu ba,” inji Ndume.
Ya ce mutane na cikin matsanancin wahala musamman ma jihar sa ta Borno.
“Mutane na cikin matsi, akwai yunwa, ɓacin-rai da kuma fushi cikin al’umma,” inji Sanatan.
Ya ce ya san shugaba Tinubu yana da manufa mai kyau ga ’yan Nijeriya, sai dai wasu masu ba shi shawara ne ke son kassara ’yan ƙasar ta hanyar ba shi shawara mara amfani.
Sanata Ndume ya buƙaci shugaban ƙasar da ya duba batutuwan da zarar ya koma daga hutun da ya tafi da nufin shawo kan su.
A ɗaya ɓangaren kuma, Sanata Ndume ya ce zai ci gaba da faɗa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo masa kora daga jam’iyyar.
Sanata Ali Ndume ya ce: “Kowa ya san abin da ke faruwa a ƙasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in gaya ma shugaban ƙasa don a kawo gyara”.
Sai dai ga dukkan alamu, ko Shugaba Tinubu bai ga laifin waɗannan kalamai ba, to ran jam’iyyarsa ta APC ya ɓaci, abin da ya sanya ta fitar da sanarwa tana yi wa Sanata Ndume gargaɗi.
APC ta nuna cewa Ali Ndume, babban ɗan jam’iyya ne kuma sanata sannan yana da ƙima sosai a idonta da kuma jama’a, don haka in ji ta, bai kamata duk lokacin da za a ambace shi, sai a ce ya yi wani abu da zai tozarta jam’iyya ba.
Ta ce an ambato sanatan a baya-bayan nan yana ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu yana zagaye da mashawarta waɗanda ba nagari ba, ko kuma ’yan hana ruwa gudu da ke toshe hanyar da za a je, a ba shi shawara tagari.
