Liverpool ta cigaba da nuna bajinta a wannan kaka a ƙarƙashin kocinta Arne Slot, abin da ya sa ta ke ta kafa jerin tarihi a halin da ake ciki, kuma nasarta ta daren ya ci gaba da nuna yadda ta shiga wannan kaka da ƙafar dama.
Liverpool ta doke RB Leipzig da ci ɗaya mai ban haushi a daren Laraba, a wasan zakarun nahiyar Turai. Leipzig na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, wanda ya bar ƙungiyar bayan shafe shekaru 9 zai riƙa kulawa da su a matsayinsa na jagoran abin da ya shafi ƙwallon ƙafar ƙasa da ƙasa a ƙungiyar Red Bull.
A halin da ake ciki, Liverpool ta lashe ilahirin wasanni 6 na farkon wannan kaka da ta buga a waje a karon farko cikin shekaru 132 na tarihinta, kuma Slot, shi ne koci na farko da ya lashe wasanni 11 a cikin 12 da ya jagoranta a dukkan gasa a tarihin gasar firmiyar Ingila.
Kocin ɗan ƙasar Netherlands ya riga ya kai Liverpool ƙololuwar teburin gasar Firmiya bayan wasanni 8. Yanzu nasarori 3 a jere a gasar zakarun Turai sun sa Liverpool ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da su ke da maki 9 cif-cif a halin da ake ciki.
