Babu wa’adi ga amfani da tsofaffin takardun kuɗi a Nijeriya – CBN

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban bankin Nijeriya, CBN ya yi kira ga al’umma game da batun da ke yawo na cewa tsofaffin takardun nairori na N200, N500 da N1,000 za su daina amfani nan da ƙarshen shekarar 2024.

Cikin wata takarda da Daraktar hulɗa da jama’a na bankin, Sidi Ali Hakama ta fitar a ranar Alhamis, bankin ya ce babu ƙamshin gaskiya game da labarin don haka ya ke kira ga al’umma su ƙaurace wa labarin.

Bankin ya kuma ce hukuncin da Kotun Ƙoli ta yi na watan 29 ga watan Nuwamban, 2023, ya nuna cewa za a cigaba da amfani da su ba tare da iyakance musu lokaci ba.

Sannan, bankin ya umarci bankuna su cigaba da karɓar da bayar da kowane irin nau’in takardar kuɗi da ƙasa ta amince da shi.

Saboda haka, bankin ya buƙaci al’umma su yi watsi da duk wani batu da ke cewa za a daina amfani da tsofaffin takardun nairorin a ranar 31 ga watan Disamba, 2024.

By Babaji