Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nemi Gwamnatin Tarayya ta gaggauta magance matsalar rashin tsaro da ke ƙara yadɗuwa a faɗin ƙasar.
Obasanjo ya yi magana a ranar Lahadi a fadar Rilwanu Suleiman-Adamu, Sarkin Bauchi.
Tsohon janar na sojan ya je Bauchi ne domin ƙaddamar da ayyukan tituna da gwamnan jihar, Bala Mohammed, ya gina.
Obasanjo ya ce yanayin tsaro a Nijeriya a yau yana da matuƙar “matsala”, yana mai cewa gwamnatinsa ta bai wa tsaron rayuka da dukiyoyi fifiko.
“Irin tsaron da ya fi dacewa shi ne na al’umma domin kowa ya san makwabcinsa a cikin al’umma. Tare da wannan, yana da sauƙi a gano miyagun mutane,” in ji shi.
“Yanayin rashin tsaro a Nijeriya a yau yana da matsala sosai, ba kamar lokacin da muke mulki ba, lokacin da muka bai wa tsaron rayuka da dukiyoyi fifiko a faɗin ƙasar.
“Ya kamata mu ɗauki mataki cikin gaggawa kan wannan.”
Tsohon shugaban ƙasar ya yi kira ga sarakuna da su ƙarfafa tsaron al’umma a yankunansu don magance ƙaruwar aikata laifuka.
